Saturday, 20 October 2018

Video: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 76

October 20, 2018 0

An wayi gari Adama da Kyauta Dillaliya sun sha alwashin zubar da cikin Hannatu ko ta halin kaka, bayan da suka hadu da wani Likita daya kware wajen zubar da ciki. Sai dai Hannatu ta ki amincewa. amma duk da haka Adama ta tursasa ta ba a son ranta ba, suka tafi wajen zubar da cikin. Sai dai sakamakon karshe ya bar baya da kura...

Download

Monday, 15 October 2018

Hausa Novel: Bugun Zuciya ( By Fadeela Lamido )

October 15, 2018 1


*BUGUN ZUCIYA*
   ( _Heartbeat_)

                   馃挀馃挐馃挆
                        馃挆           

馃挀馃挐馃挆
*By*
     馃挆
    _*Fadeela Lamido*_

         
        1鈨� to 3鈨�


*Dasunan Allah Mai Rahama maijin kyai*
馃摍 Dada! Dada!! Wata matashiyar yariya ce ke rangadawa tsohuwar kakanta kira"

    Fitowa tsohowar tayi tana kokarin gyara daurin zaninta take fadin, nashige su nikam wannan irin kira haka?"

    Turbune fuska yariyar tayi lokacin da sukayi ido biyu da kakar tata tana fadin ayya dada danma kinsamu ina murnan ganinki shine zakice wani kin shigesu?, juyawa tayi da nufin komawa, cikin sauri dada ta jawota cikin fara'a tace dawo2 ai ban dauki murya ba, maraba lale lale takwara, karashewa tayi tare da jawota jikinta ta rungume"

     Daidai lokacin wani farin dattiju ya shigo tare da sallama, yana ganin su haka yasaki murmushi"

    Cikin sauri yariyar ta kwace daga rukon dada ta nufi cikin dakin, tabarma ta dauko ta shinfida wa mahaifinta ya zauna tana jin sun shiga gaisawa da dada ta koma dakin dada"

    Gyarawa tashigayi duk da cewa dakin agyare yake dan dada macece me matukar tsafta, gadon ta lokuikuye yayi tsaf kaman baza ahauba sannan ta dau tsintsiya tahau shara"

    Bayan ta gama ne ta dauko dan kaskon turaren wuta ta nufin dan karamin kitchen din dada dake tsakar gida"

     Tagabansu dada tazo zata wuce dan haka duk suka juyo suna kallonta harta kusa isa kitchen din dada tace"

    Aiko takwara bazaki samu rushi a kitchen dinnan ba, dan yanzun baban ninki sun hanani amfani da murhu"

    Juyowa tayi ahankali tace to yanzun baki kunne turaran rushi kenan?

    Gurin tabawa nake samowa"

    Cikin rawar jiki ta nufi kofar gida tana fadin bari naje na samo"

   Lokacin da dada ta komar da kallonta ga dannata gani tayi yayi shiru kanshi akasa, gyaran murya tayi sannan tace girman dan mutum babu wuya yanzun dan Allah kalli yadda takwara ta girma ko yanzun aka mata aure saita xauna"

    Da sauri ya dago kai, yace dada kin sosamin inda ke min kyaikayi, hankalina ya fara tashi ayau tum muna hanya zuciyata ta fara tsinkewa"

   Cikin kulawa tace kakwatar da hankalin ka insha Allahu Allah zai tsare babu abin da zai faru, kuma ma ai takwarar tawa Allahamdulillahi natse take tsaf ga kunya ga tsafta"


     Hmmm dada akwai wani hali dana kula tanashi wadda har yanzun banji kowa ya furta ba, ban saniba koni kadai nake gani?

   Kaga, banason jajibe2 karkace komai tunda ta gama secondary data same miji amata aure, idan ma kana da burin tayi karatu ne idan tayi aure tayishi can dakin mijinta"

   Nisawa yayi daidai lokacin ta shigo da sauri tashige dakin dada cikin kankanin lokaci kamshi ya cikka gidan"

    Dada ko hira sukaci gaba da danta zuwa can ya dauki mukullin motar sa dake kan tabarma yayiwa dada sallama ya fice"

    Mikewa dada tayi ta nufi daki tana fadin takwara maza ki fito kutafi kisan abbanki besan jira"

    Aguje ta fito ranta bace ta kalli kakar tata tace kai dada memakon kice mishi yabarni anan, ninafi son zamagurin ki kuma, shiru tayi kawai ta nufu kofa cikin zubura baki"

    Binta da kallo dada tayi harta kule, sannan ta sauke idananunta tare da fadin duk sanki da gidan nan *Asma'u* dole ki hakura dan babanninki ba yadda zasuyi ba"

    Ko da suka kama hanya babu abinda take banda zunbura baki, abbanta na kula da ita saidai ya dauke idon daga kallon ta dan ya fahimce manufarta"

    Suna isa gida ta nufin dakin mahaifiyarta ranta bace, tare da matso hawaye"

    *Ma'u* ya, kin fita da farinciki kuma kin dawo min da kuka, menene ya faru?

    Turo baki ta karayi cikin kuka tace mama nifah banason gidan nan nafison gidan dada, kuma aidama keda abba kuncemin idan na kare secondary zan koma can"

    Shiru mama tayi tana nazari kafin ta dago kai abba yayi sallama ya shigo ganin su haka yasashi hade fuska tare da fadin yaya ne?

   Mikewa mama tayi tare da fadin alhaji ai kafi kowa sanin halinta gatanan wai ita gidan hajiya takeson zama"

   Bazaiyuwu ba mamana, idan kikayi wasa konan da kofar gida zan hanaki fita, kinga yau kika dawo daga makaranta karki yadda wani abu ya hadani dake ban ce bazaki koma gurin dada ba, amman sai naga yanayin natsuwar ki, yana gama fadin haka ya fice abinsa ko waiwaye babu"

   Washegari


  *Asma'u* ce tsaye gaban mama cikin shirinta na tafiya islamiyya jan wando farar riga tare da jan hijjabi kudin break mama ta miko mata sannan ta mata sallam ta fice"

   Gidan kawarta Zainab ta nufa cikin sauri dan karta wuce ta barta"

     Tana kokarin shiga gidan zainab na fitowa cikin farin ciki suka rungumi juna cikin dauki zaina ke tambayan ta yaushe kika dawo?

   Jiya abba ya dauko ni, jawo hannunta tayi tana fadin zo mutafi idan mundawo mayi hirar danni tsoron bulalan baba idi nake"

    Mike layin sukayi har sun kusa isa makarantar zainab tajawo hannun *Ma'u* tanufi wani dan lungu"

    Cijewa *ma'u* tayi tare da fadin me zamuyi alungu kuma?

    Cikin rawar jiki tace *ma'u* taho dan Allah kinga waccen, na zaune din cen, dan daba ne idan yana zaune agurin ko maza basa wucewa, kizo mu wuce tunkan ya hangu mu"

    Hannu *ma'u* ta daga ta nunashi tare da ya tsuna baki tana fadin waccen din?

     Bege hannunta xainab tayi tace ke *ma'u* wlh idan yaga kina nunashi munshiga uku, gudun tsiya ne dashi kuma jikin shi duk wukake ne, ranan fa muna aji muna karatu saiga baba idi aguje, sai haki yake wai duna ne ya biyoshi"

     Tintsirewa *ma'u* tayi da dariya hartana rike ciki, ganin haka yasa Zainab ta sake ta arude takoma jikin wani gida ta labe"

    Tsagaitawa tayi da dariyar sannan tabi bayan zainab kallonta tayi tace gaskiya ke muguwar matsoraciya ce nikam bebani tsoro ba, dan haka wlh ta gabanshi zan wuce, ai layin bana ubanshi bane dazai hana mutane wucewa dallah fito mutafi"

       Fitowa zainab tayi daga mabuyarta tana share zufah, dariya *ma'u* ta kara tutsirewa dashi sannan ta kama hannun zainab tana fadin to meyasa akecemishi *Duna* kuma gashi ba baki bane?

   Oho nima haka naji anacemai *Shamsu duna* tafiya suka fara dan haka kowaccen su ta tsuke bakinta"

     Lokacin dasuka isa dafdashi zainab ta sunkuyar da kanta kasa tare da sauri, itako *ma'u* kur tamai da ido tana karemai kallo,
dan haka zainab ta
Wuce tabarta agurin"

      Zaune yake idon shi akasa yana wasa wuka, dogo ne kakkaura bashi da haske kuma baza akirashi baki ba, gabobinshi abon tsoro ne duk sunbi sun murmurde xaikai kimanin shekara 33 zuwa da 35, tabone ajikin shi kaca2 gani tayi yana kokarin dagowa dan haka ta fara kokarin dauke kanta dai batakai ga dauke kan nataba suyi ido 4"

    Tsoro ne ya kamata sosai cikin sauri ta kalli kofar makarantar  gani tayi har ankulle wani sabon tsoron ne ya sake kamata, batai aune ba saiganin *Duna* tayi agabanta"

  Kerma ta fara dare da kara kallon wukar dake hannunta sai kyalli take, ahankali taxame tasa gwuiwanta akasa cikin rawan baki tace * yaya shamsuddeen inakwana?

   Hadiye wulakancin daya tanazo yayi tare da tsareta da ido"

    Cikin daure fuska yace mike"

 Da saurinta ta mike tana kokarin wucewa"

   Zonan taji ya fada dawowa tayi ta tsaya tare da runtse ido dan tunda ya matso kusa da ita tagane jikinshi abun tsoro ne gashi babu rigar kirki ajikin shi"

   Ta dade ahaka ganin da tayi baya da niyan mgn yasata bude idonta, mamaki ne ya kamata dumin hangoshi tayi ya koma gurin zaman shi idon shi lumshe kaman me bacci

    Aguje ta karasa makaranta jikinta sai rawa yake, abakin gert din ta tsaya ta saita kanta sannan ta karasa cikin mkrntr, office din baba idi ta kalla tare da addu'a Allah yasa baya ciki dan tana masifan tsoron dorinar shi, tsuguna wa tayi ta cire takalmanta ta fara takawa ahankali sadaf2 harta wuce office din tashege ajinsu"

     Saidai duk abinda take baba idi nadaga can gefe yana kallon ta hannun shi rike da buta dan yagama alwala kenan ya mike ya hangota tana sanda"

    Kai ya girgiza sannan ya shiga tunani yariyar nan batajin mgn duk da cewa mahaifinta namatukar kokari wajen bata tarbiya, dukanta yaso yi sai dai yasan halin *Asma'u* da tsoron duka dan ta makalkaleshi bawani abu bane awajenta, dan haka gara kawai ya barta"

   Karfe 11:30am aka tashesu sai dai ana buga kararrawan baba idin ya aiko akira masa *ma'u*

    Hankalinta be tashiba kawayenta taja su uku suka isa gurin baba idi"

    Hango fuskanshi kawai sukayi su kasan lallai babu wasa dan haka duk suka doje"

    Haushi sosai *ma'u* taji ahankali ta fara takawa harta isa gabanshi"

     Cikin girmamawa ta gaidashi sannan ta sunkuyar da kanta kasa"

    Ke *Asma'u* karfe nawa kikazo makaranta?

     yau?

Kinci gidan Ku, ai Ina kallon ki sanda kikazo, meya yahana ki zowa makaranta akan lokaci?

     Um um baba wlh daman yaune abban mu ya daukoni daga makaranta yanzun fah ko gida banje ba......

  Sakin baki baba idi yayi yana kallota yarasa ma me zaice mata shiru yayi yana kallon kasa zuwa can ya dago yace"

    *Asma'u* yau yaushe?

 
      Alhamis"

   Cikin ido baba idi ya kalleta

     Ganin haka *ma'u* ta fara girgiza jiki alman tsoro, runtse ido baba idi yayi domin gani yayi kirjinta na tsalle, addi'oi neman tsari yayi sannan ya bude ido yace"

    *Asma'u* ? Ki kace yau alhamis?

     Shiru tayi dan haka ya girgizakai sannan yace Allah ya shirye ki"

Harta fara tafiya taji muryan shi yana cewa, ai zanga baban naki"

     Tsurrr cikinta ya kada, cikin sauri ta juyo ta tsuguna tare da fadin me kace?

   Jeki kawai ba dake nake ba"

    Marai2 cewa tayi idonta cike da hawaye tace baba dan Allah karka gayawa abba wlh daga yau nabari"

    Shiru kawai yayi yana kallonta dan becika son yin dogowar magana da itaba duk da yariya ce karama tana matukar birge shi saboda saurin kadaukan karatu da anbiya data dauke shi, kiriniyarta kawai ke hada shi da da ita domin duk fadin makaranta bawanda besan da zaman *ma'u* ba sabo da tsokanar tsiya"

     Kara daure fuska yayi sannan yace naji tafi"

    Jikinta asanyaye ta isa gurin kawayen ta dasukayi tsaye bakin mkrntr suna jiran ta, dan duk daliban sun wuce suka dai suka rage"

    Tana shiga cikin su ta manta da zancen wani baba idi, lbrn haduwanta da *Duna* ta fara basu"

     Rahama da faty ne sukaita kwasan dariya dasukaji *ma'u* ta tsugu ta gaida *Duna* itako zainab kara rudewa tayi cikin sauri ta nufa lungun da taso bi dazon tana fadin nidai saikun taho"

     Basu hanataba tafiya suka fara suna cigaba da zancen *Duna*"

    Rahama wai meyasa ake cemishi *Duna*?, ni naga beyi bakin da za'ace mishi haka ba, ni fuskar shi wlh kyau tamin jikinshi ne kawai yabani tsoro"

    Au ke har kallon faskan tashi kikayi ni bantaba mai kallon kurullah ba dan baya son a kalleshi, amman naji mutane na cewa wai *karan* shi ne bakinkirin shiyasa ake kiransa *Shamsu duna*"

    Hannun Rahama ta rike sannan tace toh wai meyasa baya son akalleshi?

    Oho nima bansani ba"

    Faty ce takalli *ma'u* tace kefa kin cika tambayan tsiya idan kin matso kije ki tambaye shi"

  Murmushi kawai *ma'u* tayi, shiru sukayi harsuka isa gurin da ta ganshi daxun sai dai yanxun babu kowa agurin, raba ido *ma'u* tafara duk ta waiga babu alamansa, cizon yatsa tayi  sannan tacigaba da tafiya

    sun wuce gurin da kadan suka hango shi jingine jikin wani gida ya rufe fuskan shi da hula, da alama bacci yake"

    Cikin sandan suka wuce shi, ja *ma'u* tayi da baya tare da fadin kash馃槵 na manta xobe na aji kuxo ku rakani na dauko"

    Faty ce ta bata fuska sannan tace gsky kibari da yamma kyaduba"

    Sakin hannun Rahama *ma'u* tayi sannan tace kuje sai nazo dan bazan iya zuwa gida babushi ba, abba na ne fah ya sayomin shi a Dubai"

     Da haka tamusu wayo ta koma baya sai da ta bari su Rahama suka bace da ganin ta sannan ta tsuna ta debi dutsinan ta madaidaita guda 3  a hankali take takawa  jikin gidan dake kallon shi ta nufa ta shige dan wani lungu dake tsakanin gidajen guda 2 ta labe, dutsen ta daya ta dauka sannan tayi saitin *Duna*     


    _Heartbeat_
*Mmn Yazeed*
[24/01, 11:03 a.m.] 鈥�+234 906 689 6652鈥�: 馃挆馃挐馃挐馃挆
鈥�*BUGUN ZUCIYA*鈥�
   ( 鈥婬eartbeat鈥�)

                   馃挀馃挐馃挆
                        馃挆           

馃挀馃挐馃挆
鈥婤y鈥�
     馃挆
    鈥嬧€�*Fadeela Lamido*           4鈨� to 6鈨�
馃摀 Bakaramin firgita ma'u tayi ba lokacin da taga duna ya bude hannun shi ya cabe dutsen, cikin sauri ta sunkuyar da kanta dan gudun kar ya hangota"

    Shiru taji dan haka ta sake lekawa, baccinshi taga yaci gaba kamar ma bashi aka jefa ba, tintserewa ma'u tayi da dariya tare da fadin ashema magagi yake, katon banza baccin rana harda magagi, dariya ta kara sannan ta sake daukan wani ta jefa mishi"

     Wannan karon ahancin shi ya sauka amman ko motsawa beyi ba"

    Bakaramin dariya ma'u ke kwasa ba saida tayi me isarta sannan tace kash馃槵 ina ma na taho da waya dana mai photo nakaiwa su zee suga mutumin da sukejin tsoron sa ashema nauyin bacci gare sa harda su magagi"

     Wani dutsen ta sake dagawa, jin kiran sallah yasata zabura ta yarda dutse ta fito cikin takun kasaita ta wuce deeni tana kwambare kafada"

      Sai karfe 1:15 ma'u ta shiga gida, da fada mamata taryeta tana fadin"

     Asma'u wanne irin kunne gareki dazun2 nan abban Ki yace kidaina biyawa gidan dada amman dayake kunnen ki na kashi ne saida kikaje ko?


    Muryanta dauke da shagwaba tace, mama nifa bacan naje ba, tun dazun fah muna makaranta baba idi ne yasamu sharan masallaci"

    Fuskan mama dauke da rashin yadda tace sharan masallaci? Tsohowa bansan karya inace maza keyi?

    Tun yaushe aka daina basu, ai basu iyaba duk ranan da maxa sukayi baya sharuwa muko namu yayi kyau sosai malamai nata samana  albarkan Allah ya bamu miji nagari"

     
    'Da da mahaifi sai Allah, nan danan mama ta saki murmushi tana ameen  tsohowa Allah ya mike albarka"

    Cikin kunya tace amin sannan ta nufi dakinta"

     Kai tsaye toilet ta shige, wanka tayi sannan ta fito rike da kayan da ta cire tana kwalah kira goggo tani2

    Da saurinta ta shigo dakin tare da fadin Asmau lfy kuwa?

   Kayan ta mika mata tana fadin lfy lau goggo kayan mkrnt na zaki wanke min"

     Toh kuma gashi yanzun bani nake wanki ba, bala ne keyi amman bari nakai masa"

     Yar karamar riga ta saka tare da siket daidai guiwar ta, fitowa tayi tana tafe tana raira karatun al Qur'ani, afalo ta samu mama, cak ta tsaya lokacin da ta hango kayan makarantar ta agefen mama"

    Agogo ta daga kai ta kalla 2:10pm cikin fushi tace mama kinga goggo tani nabata kayan.....

    Dakatar da ita mama tayi da fadin nina hanata takaiwa bala kayan, goggon sa'arki ce ita dazaki dinga kwala mata kira kina danga daki, saikace sabowar mejego?

    Shiru tayi tana cigaba da zonburo baki"

   Mama taci gaba da cewa toh maza ki dauki kayanki kije ki wanke dan goggo tunda tayi ciwon hannu abban ki ya hanata wanki,  bala ne keyi, kuma ma bandan rashin hankali irin naki ya zaki hado harda bra dinki kice wai akwaiwa bala, yanzun ke bazaki iya wankewa ba acikin toilet"

    Mama nifa wlh abani duk wani aiki amman banda wanki" ni ban ma iya ba wlh"

    Toh aiko zaki koya maza ki kwashe kayan ki kije ki wanke babu me wanke miki agidan nan"

     Buga kafa ta fara akasa tare da kara kallon agogo cikin kuka tace"

   Mama nifah inason ne naje mkrntn yamma Kuma gashi yanzun lokaci ya kure, kuma idan banje yau ba duka na za'yi gobe"

   Karfe nawa kika shigo gidan nan?, ai suma malaman sunsan yau bazaku samu zuwa ba, tun da su suka saku aiki"

    Juyawa kawai tayi ta koma daki, dan bata da bakin mgn, kan gadonta ta fada, murmushi ta sake lokacin da ta tuna baccin duna, tare da wassafa fuskanshi a idon ta, mutun ne kyakyawa sai dai yaya akayi ya saka kanshi adaba, gashi duk anji mishi ciwo ajiki, da alama ma  bashi da karfi tunda yake bari na jimai ciwo, tsaki taja tare da fadin katon banza kana Yawo da wukake amman kana bacci atiti badole ayanyanke ka ba"

   Washegari tun karfe 7:30 ta nufi mkrnt bata biyawa zainab ba dan tasan bazata barta tai abinda tayi niyya yadda ya kamata ba"

     Tafe take cikin kayan mkrnt idan ka ganta gwanin ban sha'awa, ita ba dugowa ba ita ba gajera ba, fara ce tas, ga wani siririn hanci da bakin ta madaidai ci shekarunta basu wuce 16 zuwa 17 ba  amman kirjinta cike yake kai kace wata cikkakiya budurwa ce"

    Lokacin da ta isa kofar gidan da taga duna dubawa tayi ko ina babushi babu alamar sa, azuciyar ta taji babu dadi dan taso ace ta ganshi"

    Kad'a kai tayi ta wuce mkrt har aka tashi bata cikin natsuwar ta, Allah2 take atashi tabi hanya"

     Tana ganin akusan tashi ta tsiri rubutu, dan haka su rahama basu tsaya jiranta ba sukayi
tafiyan su"

    Saida ta dainajin hayaniyan yan mkrntr sannan ta dauki littafinta ta fito"

    Dakalin ta da ta ganshi akai jiya yauma yauma kwace yake agurin ya daura kafarsa daya kan daya, ya daura hula kan fuskar"

    Babu kowa alayin dan unguwa ce ta masu hali kowa yana cikin gidan sa babu ruwan wani da wani, hakan ne yaba ma'u daman isa gaban duna cikin sanda"

    Cikin siririyar muryanta ta rangada sallama taji shiru babu amsa dan haka ta gara matsawa daf dashi tare da tabbacin yauma baccin shi yayi nisa kaman jiya, ahankali ta daga hannuta ta dafa hular dake kanshi, jitayi be motsaba dan haka ta daga hular fuskan ta bai yana"

    Idon shi  rufe dan haka ma'u ta bude baki da hanci tana karemai kallo"

    Deeni wankan tarwada ne dan baza akirashi baki ba yana da duguwar fuska tare da dogon hanci daidai gwargwado, sakko da idonta tayi kan kirjishi da tat bai su kai kaca kaca dashi, yatsa ta cija sannan tace afili, meyasa kake bacci atiti bayan kuma ka sani sarai nauyin baccin gare ka, koni danake mace zan iya kashe ka ma ba jimaka ciwo ba, kallo ta kara masa sannan ta saka hannu ajakar makaranta ta dau waya ta daukeshi hoto har guda biyar sannan ta kwashe da dariya tare da fadin kai gskiya ni jaruma ce, agogo cikin wayar ta duba sannan ta nufi gida cikin sauri"

    Washegari ko ta nuna ma kawayen ta hotunan duna kaman yadda tayi niyya, mamaki ne ya kamasu tun daga ranan zee bata kara yadda ta jera da ma'u ba, dasu rahama take jerawa su jirata daga can gefe ta gama tsokanan duna tazo su tafi suna kyalkyalketa dariya"

    Ahankali wannan dabi'a tazama jiki agun ma'u kullum idan aka tashi mkrnt saita sameshi agurin yana bacci, haka zata gama surutun ta akan duna ta wuce gida"

    Haka har aka samu tsawon wata biyu ,wannan lokacin ma'u intaje gaban deeni bata sanda ko mgn ahankali dan tasan idan har yayi bacci idan kaso zaka iya daukan shi ka gudu"

    Abu ya zaman ma ma'u jiki harta kai alhamis da juma'a da babu makaran ta tana shiga damuwa dan haka yau juma'a da wuri ta isa dakin abban ta"

    Bayan ta gaida shi ta zauna daf dashi"

    Kallonta yayi da murmushi akan fuskanshi yace mamana ya akayi? duk yadda akayi akwai abin da kike so"

    Cikin shagwa ba tace abba na tuna Dada ne"

    Dada tana nan lfy mamana kulum tana cewa nagaishe mata da takwararta, ba inagaya miki ba?

     Eh abba amman ni inason ne naje naganta"

    Shiru yayi zuwa can ya dago yana share zufa yace, to naji amman kibari nasamu lokaci zan kaiki da kaina"

    Shiru tayi badan  ranta yaso ba, tana fitowa ta fara matso hawaye, karo sukaci da mama zata shiga dakin, ganin ma'u cikin hawaye yasa tabita da kallo"

   Alhaji yau kuma fada kukayi kaida maman taka?, naga ta fita tana share hawaye"

     Au kuka takeyi? Allah sarki, wlh ina matukar jin dadin yadda Asmau take nuna soyayyarta ga dada, amman kash bazan iya barinta ta zauna acan ba, sabo da gudun kar abinda ya faru shekarun baya yasa ke faruwa, shi yasa bana son na nuna mata gida biyu, kuma nacewa dada ta dawo ta zauna tare damu tace a,a bazan iya bari Asmau ta dinga zirga zirga atiti ba yau tana gida gobe tana gidan dada, dan gudun haduwa da gurba tattun samari"

    Mamace ta dago da kanta bayan ta gama sauraren shi ahankali tace alhaji Allah ne fah yake tsarewa, kuma ai be kamata ace anhanata zuwa gidan dada ba itama dadan ai bazataji dadi ba"

    Mikewa yayi fuskan shi babu annuri yana kokarin fita yace kice mata idan shirye take ta fito na sauke ta"

    Dagudu ma'u ta fito fuskanta cike da fara'a ta shiga motar ta zauna har suka isa bece mata komai ba"

    Akofar gidan ya sauketa sannan yace ki jirani idan nata so zanzo na dauke ki, ranta be soba, amsawa tayi ta shige gidan"

     Bakaramin dadi dada tajiba dataga ma'u, aikace2 gidan sukayi tare sannan suka zauna suna hira, suna cikin haka dada ta fara gyangyadi, ma'u naganin haka ta kalli agogo 11:15 tagani, zama tayi har taga 11:20 dan haka ta mike ta dauki bakin gyalenta agefen gadon dada sadaf2 ta fice"

     Da sauri take ta fiya dan taje ta dawo kafin dada ta tashi, tun daga nesa ta gane baya nan, dan gurin da yake kwanciya babu komai awajen, ja tayi ta tsaya domin taso ace ta ganshi"

     Gajiya tayi da tsayowa dan haka ta juya ta fara tafiya da nufin komawa gida, kaman ance ta juya ta hango shi kwace, kai yaya akayi haka? Ma'u ta tambayi zuciyarta, juyawa tayi cikin sauri ta isa gurin tare da sallama, jin babu amsa ya tabbatar mata da bacci ya wuce dashi daf dashi taje ta cire hular dake fuskanshi, idonshi rufe yake kamar kulum, fuskanta takai saitin tashi sannan ta huramai iska ahankali"

     Wani gwaron ajiyan zuciya ya Saki, da sauri ma,u taja baya"

    Ganin yaci gaba da baccin yasa ta sake matsawa ta bude baki ta sake hura mai fuska akaro na biyu, karaf taji anrike ahannunta"

     Subuhanallah yau nashiga uku na lalace, wayyo abba na waiyo dadata kuzo ku ceceni, dan Allah kayi hakuri

wlh takalmi nane ya tsinke na tsuguna zan dauka bansan akwai mutum agurin baHeartbeat
Mmn Yazeed馃崄鈥�
[24/01, 11:03 a.m.] 鈥�+234 906 689 6652鈥�: 馃挆馃挐馃挐馃挆
鈥�*BUGUN ZUCIYA*鈥�
   ( 鈥婬eartbeat鈥�)

                   馃挀馃挐馃挆
                        馃挆           

馃挀馃挐馃挆
鈥婤y鈥�
     馃挆
    鈥嬧€�*Fadeela Lamido*              7鈨� to 9鈨�
馃摎 Murmushi yayi kadan batare da yace komai ba, binta da wani mayan kallo kawai yake"

   Ma'u ko duk ta firgice tana rokon shi ya sakar mata hannu"

    Mikewa yayi tsaye batare da ya saki hannun ba, kuma har yanzun idonshi na kanta wani maya tatcen kallo yake mata"

     Cikin wata irin murya da bazata iya tattance yanayin sa ba yace"

    Ke baby natsu, bason gaddama, kishiga hankalin ki, kinji ko?

    Hannunta tasa duk 2 ta rufe bakinta tana daga kai alamar eh, acikin zuciyarta ko fadi take tawa ta kare"

     Menene sunan ki?

    Cikin rawar baki tace Asmau"

    Lumshe ido yayi sannan yasa ke cewa menene ya fito dake yau bayan babu mkrnt?

    Dan Allah dan darajan annabi kayi hakuri wlh daga gidan kakata nake, nasan yanzu tanacen tana nema na"

    Cikin wata irin murya yace baruwa na da wata kakarki ni ke kadai nasan.....

    Kukane ya kwace mata, cikin kukan tace to aini ban sanka ba wlh tsautsayi ne kawai ya kawoni nan, wlh da nasan haka ne da banzo ba"

    Murmushi ya sakeyi ahankali ya kara runtse hannuta cikin nashi, tare da lumshi ido"

    Zuwa can ya bude yace inace kinzo gadi nane?, dan kada abokan gaba su kawamin farmaki, dan kinsan nifa nauyin bacci gare ni, ke fah?

     馃槴 Nima inada shi wlh, narantse inada shi"

     Wannan karan saida yadan dara sannan ya dan jawota jikin shi tare da fadin baby ki kwantar da hankalin ki, bazan miki komai ba, jarumtar ki ta birgeni, ni jarumi ne dan haka inason naga mace jaruma, kin yi kokari sosai dakika tunkare ni, amman meya hana kika kasa hakuri zuwa gobe asabar kika fito yau?

    Ainace maka gidan kakata naje yanzun ma tsautsayi ne ya fito dani"

     Hmmm kawai yace sannan yaja hannuta zuwa gurin kwanciyar shi ya zaunar da ida"

   
     **

  Aban garen dada kuwa da misalin 12:09 sallama alhaji  ne ya tasheta daga bacci"

     Afirgece ta tashi tana fadin takwara shine baki tasheni baccin ba bayan kinsa ina tafiya masallacin juma,a da wuri"

     Gaba dayan su wurga ido suke suga ta ina ma'u zata bullo daga abba har dada"

     Jin shiru yasa dada ta shiga kwala mata kira taji shiru, mikewa tayi azabure tana fadin zoka zauna inaga ta shiga gidan tabawa bari nakirata"

     Zama yayi kamar yadda dada tace sannan ya cire hular kansa ya aje agefe, tare da fadin Hmmm Allah ya kyauta"

    Lokacin da dada ta shiga gidan ta bawa cemata tayi ko kallita bata gani ba, dan haka tayo waje hartana tuntube"

     Azauren suka hadu da dan tabawa yana kokarin shiga gidan, kallon shi dada tayi tace kai iro baka gamin Asmau ba?

    Aiko dazun naganta nan wajen hanyar mkrtnr su......

   Bata bari ya rufe baki ba tabi hanya tana gudu2 sauri2"

    Kalu innalillahi wa Inna ilaihir raju'un ta fada lokacin da ta hango ma'u rike hannun Duna"

    Jikintane ya fara rawa bata San sanda ta kwasa aguje ta nufi gida ba"
 
    Ganin dada agoje abin yabawa iro daya biyo bayan mamaki, shan gabanta yayi dan gudun karta tuntsura, riketa yayi tare da fadin dada lfy menene ya faru?

    Ajiyan zuciya ta fara bata iya cewa komai ba saijan hannun iro take"

      Daga nesa tamai nuni dasu, lokacin suna zaune ita da Duna"

    Salati yayi sannan yace dada, ki tsaya inwuce saiki kwala mata kira tunda ke tsohowa ce kila bazai miki komai ba, amman ni idan ya ganni akwai matsala dada, tunda shi fadan shi baya wucewa inda kikasan shedan haka yake, cikin sauri iro yabar wajan yana me Kara karfafawa dada guiwa da hannun shi"

     Tashin hankali ne sosai azuciyar Dada, kafafuwanta banda rawa babu abinda suke, kallo ma'u tayi tana mamakin yaya akayi ma'u tasan deeni harta bari suka zauna guri daya , kuma da alama ba tursasata yayi ba, kawar da tunanin tayi sannan ta daga murya ta kwalawa ma'u Kira"

    Tana hango dada ta mike azabure, ta nufota aguje, ganin haka duna ya mike ya biyo bayanta"

   Takaici ne ya kama dada dan haka ma'u na isowa ta daga hannu ta sharara mata mari, hannu ta sake dagawa zata kara mata, taji andaka mata tsawa cikin wata irin murya ta kyauraye"

   Ke ! Ke!! Yasin yasin kika sake hannunki ya kara kaiwa jikinta sena sassara ki, Allah wlh *gunduwa gunduwa* zanyi dake, yasin hannunki ya kara kaiwa jikin ta kigani"

   Suman tsaye dada tayi, fita tayi daga hayyacin ta, lokacin da network dinta ya dawo gani tayi suna tafe ita da ma,u sai janta take, tana kara fadin dada taho mana"

   Bata iyace mata komai ba illah binta da take da kallo, sai dai akwai tashin hankali karara a idon ma,u"

   Sauri ta kara dan sai yanzun ta tuna abban Asma'u yana gida yanajiran su, jitayi kaman lema ajikinta dan haka takai idonta kan zaninta jike yake sharkaf nan ta tabbatar fitsari ne"

    Suna karya kwanan layin, ma'u ta hango abbanta sai zagaye yake akofar gidan dada, gefen shi iro ne azaune ya rafka uban tagumi"

    Hunnun dada ta matse tare da fadin wayyo Allah na, nashiga uku"

    Kallota kawai dada tayi ta tabe baki tare da fadin Hmmm"

   Jikin ma'u ban da rawa ba abinda yake, cikin mtsanan cin tashin hankali ta taja ta tsaya tana me tsiyayar da hawaye dan ta tabbatar yau kashinta ya gama bushewa"

     Ganin abba na tahowa yasa ta faraja da baya ahankali, tana kokarin rike Dada"

    Yana isowa yasa hannun shi ya rabata da jikin dada ya zaf ga mata mari har saida ta fadi kasa, cikin karaji yace daga gidan uban wa kike?, jin da yayi babu amsa yasa ya daga kafa ya nufi cikinta yana kokarin tokarin ta aciki, tare da fadin badake nake mgn ba?

    Cikin matsanan cin firgici dada ta rike Abba da wani irin karfi da batasan tana dashi ba, tana fadin kasheta zakayi ne?, toh bismillah nunamin yarka ce, nace kanuna min ka haifa kuma ni mahaifiyar ka ban isa na aiki yar ka ba"

    Sanyi jikin Abba yayi, cikin natsuwa ya shiga bata hakuri, badan ya yarda cewa dadan ce ta aiketa ba"

    Haka dada taita fada abba nabata, hakuri da karshe da kanta tasa ma,u amota abban ta, tana cigaba da fada"


    Dada na tsaye akofar gida har motan abba ta bace, ajiyan zuciya ta sauke sannan ta juya ta shiga gida tana mamakin inda ma,u tasan deeni"

    Kulle gidan tayi da sakata domin ita har yanzun gani take kamar duna zai shigo mata gida dan ba karamin tsorata tayi ba, wanka tayi ta gyara jikinta sannan ta wanke kayan da ta cire ta shanya, aranan dada bata runtsaba data rufe ido duna take gane"

      Asmau kuwa suna isa gida ta sauka aguje tayi cikin gida"

     Binta da kallo Abba yayi tsananta me tsanani yaji acikin ransa dan haka bayan ya shiga falon ya zauna, ma'u daga daki taji yana waya yana fadi"

    *Usman* na gari ne?, toro mun shi yanzu yanzun nan, akwai matsala"

     Faduwa ma'u tayi daga kan gadon dan ta tabbatar yau sai dai buzun ta indai ta bari har ya usman ya riketa"

   
       *WAIWAYE*


    Alhaji sani haifaffen jahar Kano ne, su 2 iyayen su suka haifa, daga shi sai yayan shi Alhaji musa, alhaji sani shine mahaifin Asmau, su uku suka haifa, tare da matar sa Fatima, usman shine babban, sannan fiddausi sai yar auta asmau wacce taci sunan kakanta"

    Shiko alhaji musa Saida ya shikara 15 be samu haihuwa ba, dan haka kaninsa alhaji sani ya bashi danshi usman alokacin yana da shekara 5"

    Usman ya taso cikin gata gidan alhaji musa tamkar dan da suka haifa da cikin su, yayin da alhaji sani yaci gaba da kula da fiddausi wadda take yar shekara 2"

     Alharji sani da yayan sa ma,aikatan gwamnati ne, kuma suna samu daidai gwargwado dan a unguwar su idan xa ai lissafin masu hali baxa a kirga 5 babu su aciki ba"

     Fiddausi nada shekara 10 aka haifin Asmau, tun daga kan asmau basu sake samun haihuwa ba"

     Bayan shekara 8 fiddausi ta zama cikakkiyar budurwa meji da kanta duk abin da take so shi ake mata, saidai abu daya abban su baya barin yawo indai ba gidan dada tace zataba ba a barinta zuwa ko ina, dan haka lokacin da ta kare secondary ta samu daman tafiya jami'a ta balle bishashanta acan, ahankali fiddausi ta zama bata da abokai sai maza, haka zaka ganta tsakiyar maza ita kadai mace"

    Babu wadda keda lbrn halin da fiddausi take ciki amakaranta, dan da antashi gida take yowa dan tasan ko minti 10 takara sai ance inata tsaya"

    Ana haka maza suka fara canzawa fiddausi tunani domin ko duk abokanta kusan su 7 babu wadda baya lalubeta da sunan wasa, dan haka ta farajin babu abin da take so illah taga ta kadai ce da namiji"

    Duk abinda suke sauran dalubai na kula dasu, yayin da wasu daga cikin matan suke tur da halin fiddausi, ita kenan yau ka ganta manne jikin wancen gobe jikin waccen"

    Yauma kamar kullum tana cikin motar wani abokinta KB suna manne da juna ita da kanta ta lalubo bakin shi ta cusa nata ta, saida suka gama shagala, sanna ta gabatar mai da kudurinta"

    Murmushi KB yayi dan yasan za'ai haka, yayi mamaki ma da har aka kawo yanzun bata bada kai ba, sabo da salon da suke mata"


     Kwantar dakai KB yayi tare da fadin babu damuwa, amman fa saidai kizo muje Ki tayani kwana"

    Zaro ido tayi dan tasan zancen shi bamai yuwuwa bane, tace KB ? Kana son Abbana ya kasheni ne?

    Tsaki yaja sannan yace haba meyasa kike abu kamar wadda bata waye ba, ai dibara zaki masa"

     Bayan kwana 2 fiddausi ta kasa hakuri dan haka ta shirya tayi sallama akan zata gidan dada ta kwana"

       Gidansu KB ta wuce wadda har ya kaita da kwana adakin kb kuma har komai ya kasan ce, karfe 7:09am ta isa gidan dada da kayanta ajaka kamar yadda ta shiryu, ganin inda take tattale kafa yasa dada fadin ke lfy meya sameki kike wani tafiya saikace agwagwa"

     Akafa fah na taho dada wlh gajiya nayi"

    Ruwan wankan dada ta juye tayi wanka tare da gasa jikinta, ko karyawa bata tsaya yi ba, ta  haye  gado sai bacci domin KB be bari ta runtsa ba"

     Damisalin karfe 8 alhaji sani ya iso gidan ganin fiddausi agado hankalin shi ya kwanta"

    Tun daga ranan wannan dabi'a ta zaman mata jiki har saida ya kasance gaba dayan su 7 sun gama sanin wacece fiddausi"

     Ankwashi tsayon watanni ana haka kullum fiddausi tana hanya wata rana takan kwana gidan dada amman sauda yawa dakin samarinta take wucewa idan ko har ta kwana gidan dada toh safiya nayi zata wuce gurin samarinta, babu wadda ya lura da halin da fiddausi take ciki har saida fiddausi ta fara rashin lfy, ana zuwa asibiti gwajin farko aka shaida musu tana dauke da ciki Wata 2"


Saturday, 13 October 2018

Video: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 75

October 13, 2018 0


An wayi gari Adama da Kyauta Dillaliya sun sha alwashin zubar da cikin Hannatu ko ta halin kaka, bayan da suka hadu da wani Likita daya kware wajen zubar da ciki. Sai dai Hannatu ta ki amincewa. amma duk da haka Adama ta tursasa ta ba a son ranta ba, suka tafi wajen zubar da cikin. Sai dai sakamakon karshe ya bar baya da kura...

Tuesday, 9 October 2018

Hausa Novel: Yar Kurma ( By ESHATT SMILER )

October 09, 2018 0


YAR KURMA

GODIYA

Dukkan godiya ta ga ubangijin talikai, daya hallice ni cikin ni'mar musulunci. Ya kuma bani ikon d'aukar alk'alami dan yin karambani a kan wani tak'aitacen lamari bisa san sanin makamar aiki. Har gobe nid'in me neman gyara ce daga na  sama dani harma na k'asa nà kasantuwata k'ank'anuwa cikin harkar adabi.

Cikin takaici ta nuna Marwanatu da hannu, zuciyarta na  yi mata k'una saboda dariyar da take yi mata. A zafaffe ta kai mata bahagon duka, amma kash! Bata same ta ba ta saki wata giggitaciyar k'ara, ji kake kauuuuuuu! A kunnuwan Marwanatu. Benaziratu  ta k'yalk'yale da dariya ta buga k'afa irin na  Bebaye ta murd'a yatsu, take suka bada sauti d'as! 'Das!! Das!!! Alamun gargad'i tuni Marwa ta ranta ana kare.
      Bata jinkirta ba ta rufa mata baya, ai kuwa suka kasa a guje. In baka yi bani waje, basu samu matsaya ba sai a d'akin Hajja Yakura, bisa tsatsauyi suka zubar mata da biskin geron da ta ajiye. Ai kuwa cikin hargowa ta yo kansu, Marwanatu ta falle caraf ta kama Benaziratu."Wato ke 'yar kurma bakya jin magana ko?". Benaziratu ta turo baki, bata ji abinda ta furta ba amma bakinta da ta kala ta gane me furucinta yake nufi. Tuni ta hau tirje-tirje Allah ya bata sa'a ta k'wace a guje ta bar sashin. Kafar! Sukai karo da shi, a razane ta d'ago sukai ido hud'u dashi Baana. Cikin razana ta so kaucewa kamunsa amma ina ta makaro. Yana rik'e da ita ya shiga gidan, da salama Yakura ta d'ago tana amsa masa mamakin ganinsa a wannan lokaci yasa ta kasa magana cikin yaransu take kiran mai gidanta tana sanar masa. Bakura ya taso da saurinsa yana nuna farin cikinsa da ganin Baana. Da wannan damar Benaziratu ta kufce ta fyala da gudu, yabi bayanta da kallo yana murmushi karaf suka hada ido da Yakura ya sune kai yana shafa k'eya.
Gimtse fuska tayi ta shimfid'a masa tabarma karauni, ya zauna yana gaishe su tare da tambayar yadda ya same su. Cikin murmushi suke amsawa, shigowar Marwanatu tana kuka ne ya katse su. Cikin masifa Yakura tace"kin tsaya ta dake ki ko?" Marwanahtu tai ajiyar zuciya tana lab'e-lab'e saboda ta san mudin Yakura ta kamata duka zata sha. Saboda kullum gargad'inta ta daina bari Benaziratu na  dukanta ne. Cikin mamaki Baana yace" wace ce ?" Cikin jin haushi ta numfasa.
"Wacce ce kuwa banda Benaziratu?" Ta fad'a da gurb'ataciyyar hausar ta.
Mumushi yayi a ransa yana fad'in "yaushe Hajja zata sauya?". Shiru na  tsayin lokaci, ya yunk'ura zai mik'e " ina zaka"? Cewar Yakura. Kansa a k'asa ya furta "zan je in huta an jima in shiga in gaishe da Abbagana". Murmushi mahaifinsa yayi yace "Allah ya kaimu" k'wafa tayi taja hannun Marwanatu suka bar wajan. Daga shi har mahaifinsa murmushi sukai_.

Washegari da misalin k'arfe bakwai na  safe Baana yana zaune a dakalin k'ofar gidansu, ya hango tahowar Benaziratu tunda ta taho ya zuba mata ido. Shi dai rayuwarsa yarinyar tana birgeshi, komai nata cikin nutsuwa take yi duk da cewar tana da son barkwanci. Bai ankara ba harta k'araso ta zo giftawa ta d'aga masa hannu tana murmushi gab da zata shiga gidansu ya d'aga murya da k'arfin gaske, ya  k'wala mata kira *"Benah"*. Juyowa tayi ta murgud'a d'an k'aramin bakinta, ta murd'a yatsu suka bada sauti ta shige gidan. Yai murmushi a ransa yana fad'in "hallayar Benah tana nan". Cikin gidan ta shiga da fuskarta d'aure tai salama, duk haushin Baana ya tuk'eta nan duniya ta tsani a kirata da Benah, ganinta kawai iyayine irin na  Baana dan yaje birni karatu.

_"Ke! 'Yar kurma" aka fad'a da k'arfi daga gefanta, juyowa tayi tamkar mayunwacin zaki tana huci. Ganin Hajja Yakura sai ta sadda kanta k'asa tana gaisheta cikin gwarancinta irin na Bebaye. Matsowa tayi ta kama kunnanta ta murd'e ai kuwa ta saki k'ara saboda azabar wahala, shar k'wala ta zubo mata. "Dan ubanki me Marwanatu tayi miki jiya, da zaki sata Ku........?" Maganar ta katse sakammakon k'watarta da Bakura yayi yana bambamin fad'a.

"Ke dai Yakura kinji kunya, me yarinyar nan tai miki? Tsabar k'in Allah kin takura mata idan da kara itama 'yar ki ce"._

_"Kai! Kai!! Kai!!! Bakura dai na fad'in wannan, Allah suturi buk'wui ina amfanin sai da rai a nemo suna? Wai kai kana tunani zanso wannan abar? Hmmmm! Allah ya kiyayye had'a iri da kishiya". Wata muguwar harara ta makawa Marwanahtu, tuni ta ja hannun Benaziratu wadda take razgar kuka, kasancewar duk da k'arfi Yakura take maganar tana jinta. Kad'a kai Bakura yayi ya shige d'akinsa.

Suna fita sukai kici6us da Baana, hannun Benahziratu ya kamo yana tambayarta. Ta k'wace hannunta dan tuna abinda yai mata d'azu. Bata kula kowa cikin su ba ta warce hannunta tana kuka, kai tsaye gida ta nufa. Cikin raunin murya ya dubi k'anwarsa"Marwah me ya samu Benah"? Murmushi tayi dan taji dad'in yadda ya kira sunan. Tiryan-tiryan tai masa bayanin abinda Yakura tayi, kansa ya ri'ke yana jinjina hallayar mahaifiyarsa a ransa yana fadar" wai shin yaushe Hajja zata sauya?"............
   
_Kai tsaye gida ya shiga, alamu da yawa sun nuna tsantsar damuwarsa. Yana shiga da salama ta amsa  masa babu yabo ba fallasa, ya samu guri ya zauna. Minti biyar babu wanda yace uffan cikin su, ganin babu fuska ya yunk'ura ya bar gidan. Zuciyarsa na  zafi.

Kai tsaye gidansu Benahziratu ya nufa, cikin murmushi yai salama. Mamaki ne ya kamashi ganin Benazirahtu normal (lafiya) tana aikin ta. Mahaifin Benazirahtu ne ya fito da murmushi ya ce "a'a Baana barka da zuwa, saukar yaushe?" Ya shafa k'eya d'abi'ar da ta zamo masa jiki da murmushi yace. "Abbagana jiya da yamma nazo hala Benah bata gaya muku ba? Ta gani a jiyan". Cikin murmushi yace "kasan halin kayar ka", zama sukai suka k'ara gaisawa. Can sai ga Hajja Faanah ta fito, suka gaisa da nuni da hannu. Ruwa mai sanyi Benazirahtu ta ajiye masa cikin a kofin kushi, ta sake dawowa d'auke da babban a kushi ta sunkuya ta ajiye. Murmushi ya yi ya bud'e k'amshin manshanu ya yi masa salama, ya lumshe ido ganin biskin gero da miyar kub'ewa ga manshanu. Ai ba jinkirtawa ya sab'a hannun riga ya soma kwasar loma.
           _Can ya d'aga murya yace "Abbagana ina ce Hajja ce tayi girkin nan ba wannan ba?". Tsaf ta kalle bakinsa, ta gane furucinsa ai kuwa ta turo baki ta hau buga k'afaffu alamun shagwab'a. Gaba d'aya suka saki dariya, cikun gurbataciyyar maganarta tace "nafi matarka iyawa". Dariya suka sake yi, Hajja Faanah na  tambayar abinda Benazirahtu tace. Mahaifinta yai mata bayani da hannu._

_Bayan ya gama ta d'auke kwanukan, ya dubeta "Benah d'auko jakarki ta school (makaranta) in gani kinji", babu musu ta mik'e sai ga ta ta dawo d'auke da'ita, karb'a yayi yana duddubawa a hankali yake mata tambayoyi tana amsawa . Sossai yaji dadin yadda ta maida hankali tana karatu fiye da Marwah.Bai bar gidan ba sai gefun sallahr azahar, a ransa ya k'udiri kyautar da zai mata.
       ************
_Washegari kuwa sai gashi da dogayan riguna, dai-dai ita guda uku bayan sun gaisa da Hajja Faanah ya bata. Godiya sossai sukai masa, Banazirahtu baki yak'i rufuwa ya gonar audiga. Da gudu ta suri kayan ta nufi gidan wan mahaifinta, tun a soro take kwad'awa Marwanahtu kira. Tana fitowa ta hau nuna mata kayan, cikin murna tace "waya baki?" Babu komai ranta tace "Baana"........... Kafin ta k'arasa magana taji an warce kayan kai tsaye cikin murhun girki Hajja Yakura ta watsa su, wata giggitaciyar k'ara Benazirahtu tayi ta shid'e ji ka ke yif! Ta fad'i. Hakan yai dai-dai da shigowar Baana cikin kad'uwa ya furta.
"Benah!
Cikin kad'uwa yake girgizata yana kiran sunanta *Banah! Benah!! Benah!!!* amma kash! Shiru Malam yaci shirwa. Hankalinsa ya yi matuk'ar tashi da wani rikitacan kallo yake duban mahaifiyars. Sai dai kawaici irin na  d'a da uwa ya kasa tankawa. Surarta yai bai zame ko'ina ba sai d'akinsa, sossai yake zuba mata ruwa ta k'i motsawa. Ya kasa kunne amma bata motsi, k'irjinsa ya dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!. "Kadai ace *Benah* ta rasu"?. Ya fad'i hakan a ransa. Can ya tuno wani bayani da akai musu a wata lecture, yayin da mutum yai dogon suma. Hamdala yayi ga ubangiji, ya toshe hancinta ya bud' e bakinta ya had'a da nasa. Ya soma musayar numfashi kafin minti uku ta soma motsi, cikin sauri ya watsa mata ruwa.

_A hankali ta zuba masa ido, can ta fashe da matsanancin kuka saboda tunawa da kayanta."Baana kayana" , ta fad'a cikin gwaranci. Janta yayi jikinsa yana shafa kanta a hankali tai shiru sai ajiyar zuciya take. Sai da ya tabbatar da ta yi shiru ya d'auko chaculate ya bata, tare da alk'awarin kawo mata wasu sababbun kayan. Da murna tai masa salama ta nufi gida. Tana zuwa ta zauna ta bawa mahaifinta labari, murmushi yayi tare da bata hak'uri ya gargad'eta da kada ta gayawa Hajja Faanah komai, saboda gudun matsala. Koda ta tambayeta cewa tayi "kayan ne sukai yawa canzowa za'ayi".

_Cikin rashin walwala ya shiga gida, Hajja Yakura ta dubeshi "wai kai dan an k'ona kayan waccan nakasshashiyar *'YAR KURMAR* kake ciwa mutane kunu? Meye abun damuwa da lamarin mutanan da suke da nakasa a rayuwar su? Mtssss!" Ta ja tsaki tana gunguni. Cikin taushin murya ya dubeta._

_"Hajja ki fahimce ni koba komai *Benah* 'yar uwata ce, kuma k'abilarmu d'aya nakasa ba zaisa in nuna mata k'yama ba. Bafa laifi sukaiwa ubangiji ya hallice su haka ba, suma mutane ne kamar kowa kuma ubangiji yana kishin su yana sonsu. Haba Hajja". Ya fad'a da sanyin murya, ai kuwa yana direwa ta hau sababi, kai kace zaginta ya yi jikinsa yai sanyi zuciyarsa na  radad'i yana takaicin hallayar mahaifiyarsa.

TUSHAN LABARIN*_

_Baana d'a ne ga Alairam Modu kalmar Modu na  nufin  Muhammad kenan, Modu wanda akafi kira da sunan Bakura,saboda kasantuwarsa babba a gidansu. Kalmar Alairam na  d'aukar Alhaji ne a yaran Kanuri ko kuma Aisami wato Alhaji. Hajiya kuma sukan kirata Aisaram, yayin da . Bakura dai haifaffan garin Mai duguri ne, su biyu iyayyansu suka haifa da k'aninsa mai suna Hamza. Sun taso cikin so da k'aunar juna, mahaifinsu fittacan Malamine wanda yake koyar da d'alibai sama da hamsin.Sunansa Aisami Muktar Bunu, wanda da yawan muta ne ke kiransa Malam Bunu. Mahaifiyar su kyakkyawar mace ce mai suna Falmata a salinta shuwa ce._

_Sun taso cikin ingantaciyyar tarbiyar da mahaifinsu ya basu, mahaifinsu mutum ne mai neman na  kansa. Saboda sana'a maganin wulak'anci ce, shi kuma Kanurin mutum nan duniya ya tsani raini da wulak'anci. Haka kuma Kanuri ya tsani  'kazanta baya son rashin gaskiya da girman kai uwa uba d'aukar al'adar da ba tasa ba._


_Idan kuwa so kake ka burge Kanuri, to kayi masa kyautar gwal ko hula ko turare mazan su da matansu akwai son k'amshi. Kanuri akwai iya kula da tattalin mace tamkar k'wai, sun tsani rashin iya girki da yawan dariya. Matansu kuwa in kana son burgesu kyautar gwal da mindil. Mindil wani gyala ne na bare-bare, shigar su kuwa mata sunfi yin shigar lafayya, ko riga mai dogon hannu da mindil. Tsofaffun cikin su dama wasu cikin matasa, da yawa suna cin goro.Suna amfani da wani abu mai suna; ingwargo abun yana nan green ne(kore) in suna cin goro suna goge bakin su dashi don hak'orin su ya yi ja.Idan na  tsaya yi muku bayanin Kanur sai mu kwana, saboda suna da al'adu daban-daban ababban sha'awa._

_Malam Bunu yana sa'ar d'inkin hula, sai kuma d'an hasafi da yake samu daga masu zuwa ayi musu adu'a. Hakan baisa zuciyarsa ta mutu ba kullum burinsa yaransu sui karatu domin gobansu._

_Yaransu na samun kulawa dai-dai gwargwado, sun tsaya kan tarbiyar su. Kaf d'insu sai da suka hadda ce alk'ur ani mai girma sannan suka saka su a makarantar boko. Lokacin Bakura nada shekaru goma cif, Hamza kuwa nada bakwai, sai dai mahaifinsu na yi musu lesson a gida wata rana kuma Falmata tayi musu, wadda suke kira Hajja.Fanin ilmin boko ma babu dama, sun tsaya tsayin daka da karatun su. Bakura na  primary four Hamza na  primary two wani muhimmin al'ammari ya tasowa Alairam wanda hakan ya tilasta masa tashi daga Maiduguri zuwa garin biu d'aya daga k'aramar hukumar jahar Maiduguri._


_Al'amarin ya samo asali ne na wata makaranta
da aka bud'e ta islamiyya a garin biu dan
bunk'asa harkar ilmin addini. Aka d'auki Malam
Bunu zuwa wannan sashi, da farko ya soma
zuwa ya dawowa iyalansa duk mako d'aya wato
kwana bakwai. Daga baya yaga rashin dacewar
hakan, saboda yadda sukai sabo da iyalansa
shawarar Falmata ya nema ya samu k'aramin
gida ya sai musu suka koma can da zama gaba
d'aya. Dama ba wani dangi ne da shi sossai ba
duk sun mutu sai k'anin mahaifinsa guda d'aya
shima ya tsufa sossai. Haka suka tattara suka
koma._
************
_*GARIN BIU*_
_Garin Biu na d'aya daga cikin k'anannan
hukumomin jahar Maiduguri.Shi dai k'auyen Biu
k'auye ne babba, wanda Allah ya a zurta su da
noma da kuma karatu.Sun d'auki karatu da
muhimmanci fiye da yadda mai karatu yake
zato.Shiya sa suka samu cigaba a cikin
Maiduguri, dama wasu garuruwan a cikin
Maidugurin. Idan kika cire ma'aikaci d'aya na
biyu zaki ga babur ne wato yaransu. Ilahirin
mutanan biu babur ne.Haka kuma ta b'angaran
noma, Mata suna yi Maza suna yi. Amma duk da
wannan noma, dole yaro sai ya bawa karatu
lokacinsa. Suna noman gyad'a masara da
barkono da kuma gauta._
_Mutanan garin sun iya zaman duniya da kissa,
da kuma wayo sai dai suna da rowa. Sanan kuma
hanyar zuwa biu bata da kyau akwai gargada a
hanyar. Allah ya horewa mutanan Biu iya
soyyaya, sun iya soyayya 'yan garin. Matan garin
kuwa suna da had'in kai tsakanin su.Mai karatu
kar kayi mamaki in nace maka, zaka ga mace ba
abinda take b'oyewa mijinta komai tare
suke.Suna tanadi da tattalin junan su._
_Idan kuwa ka shiga jami'ar Maiduguri zaka riski,
gungun d'alibai 'yan garin har taron su suke duk
k'arshen wata. Sukan yi had'in guiwa wanda ba
shi da kud'i su tara masa.Kishi da jinsin Kanuri
akwai wahala, ballantana kishi da matan garin
Biu.Kishi da su yana da wahala saboda suna da
bala'in kissa da iya kula da Miji uwa uba
biyayya._
_Wannan shi ne bayanin garin Biu a tak'ai ce,
kuma mudin akai hutun makaranta lokacin
damuna to zaki ga d'alibai mazauna Biu na
turruruwar zuwa yin noma garin su._
_Komawar su garin Biu bai kawo nak'asu a
rayuwar su ba, hasalima cigaba suka samu ta
fannoni da dama. Makaranta mai zaman kanta
mahaifinsu ya saka su, sab'anin da da suke zuwa
makarantar gwamnati.Zama suke cike da
walwala da jin dad'i, a jikin gidan su akwai
mak'ota guda biyu d'aya 'yan garin Gwaza ce
yaranta biyu d'aya sunan sa Alangubro d'ayar
kuma Aysa. Aysa na nufin Aysha, Alangubro
kuma ranka ya dad'e.Akwai kyakkyawar alak'a
tsakanin wannan mak'ota. A hanun daman su
akwai wata dattijuwa mai suna Hajja Faanah.
Hajja Faanah mace ce mai yakanah da son yara,
tun tarewar su jininta ya had'u dana Hamza
sossai. In babu makaranta nan yake yini suna
hira tana koya masa yaran su. Hajja Fannah a
salin sunanta Fatima ne, bata da yara d'anta
d'aya hamshak'in mai kud'i ne. Ya wadata ta da
komai, yana zaune a garin Gaidahm shi da mai
d'akin sa da 'yar su guda d'aya mai sunan
Hajja.Amma kash! Kurma ce haka aka haife ta
bata magana sai dai nuni da hannu. Lokaci-
lokaci suna zuwarma Hajja hutu.Kullum Hajja
cikin bawa Hamza labarin Faanah take, hakan ya
dasa masa zumud'in san ganin ta._
_Yawan bawa Hamza labarin Faanah yasa yake yawan yiwa Hajja Faanah maganarta.Tare da tsananin tausayinta a ransa, musamman da ya samu labarin kurma ce. Badan Hajja ce ta gaya masa ba da ba zai yadda ba, saboda yadda yake ganinta a hoto kyakkyawa ce sossai. Ya matsu ya ganta,kullum Hajja cikin bashi baki take saboda basa garin kwata-kwata suna Canada can Faanah take karatunta. Kwanci tashi Bakura ya gama makarantar gaba da primary lokacin Hamza na aji biyar, Malam Bunu ya sama masa admission a jami'ar Maiduguri fanin Islamic. Haka suka cigaba da rayuwarsu abin sha'awa, Hamza na mataki na biyun  k'arshe  mahaifinsu ya rasu, sakammakon annobar amai da gudawa._

       _Mutuwar ta girgiza su sossai, Hamza sai da yayi sati a kwance a asibiti. Cikin k'ank'anin lokaci suka zama abun tausayi, Hajja Faanah ce take taimaka musu da abinci da hidimar yau da kullum.Tilas Bakura ya hak'ura da karatu ya rungumi noma, saboda tallafawa rayuwar su. Kwanci tashi Hamza ya zana jarrabawa, ta fito ranar Hajja har walima ta shirya masa.Bayan watanni biyar sakammakon sa ya fito, sakammako yayi kyau sossai Hajja da kud'inta ta sama masa gurbin karatu, a jami'ar Maiduguri. Lokaci zuwa lokaci yakan ziyarci garin Biu, hakama Maiduguri wajan k'anin Kakansu.Haka ma lokacin noma yakan zuwa sui noma  ya koma .Hamza ya dage karatu yake sossai yana karantar fanin kunne.Kullum Falmata na nunawa Bakura da Hamza su rik'i Faanah da muhimmanci ko bayan ranta. Bayan shekara d'aya  da rasuwar Malam Bunu lokacin Hamza na level one kwatsam, Hamza na zaune a gidan Hajja Faanah suka ji salama. Hajja ta mik'e tana murna cikin yaransu tana raira wak'a abin gwanin sha'awa ta rungume wata kyakkyawar mace tamkar balarabiya. Cikin kulawa tace._
_"Barka da zuwa, barka da zuwa". "Da alamu dai bak'in na musamman ne", Hamza ya fad'a a ransa. Karaf idonsa ya sauka a kan namijin da yarinyar kusa dashi wadda bata gaza shekaru goma sha hud'u  ba. Murmushi ya sub'ucewa Hamza saboda, ganin Faanah yau bayan tsayin lokacin da Hajja tai tana bashi labarin ta._

_Zahiri ya santa a hotunan ta wanda suka cika d'akin Kakarta, cikin murmushi ya dubi Hajja yace"yau dai naga takwarar Hajja". Gaba d'aya hankalinsu ya dawo kansa, cikin murmushi mahaifiyar Faanah tace._
_"Hajja wannan waye"?._
_Hajja tai murmushi, "sunansa Hamza mak'ocin mune d'an wajan Malam Bunu da nake baka labari a waya. Cikin murmushi yace"Masha Allah" bayan komai ya lafa suka zauna, ana ta hirar yau sha gamo. Hamza ya mik'e yana murmushi, yaiwa Hajja salama zuwa gida_

_Cikin walwala ya shiga gida yana bawa Hajja Falmata labari, cikin farin ciki tace "yau dai buri ya cika an ga Fauna", murmushi ya yi shigowar Bakura ya katse musu hirar da fara'a yake tambayar abinda ya faru. Hajja ce take bashi labari, da murmushi yasa hannu a aljihu ya fito da kud'i naira dubu biyu."Maza je kayo cefane a sauki bak'i", dan dad'i rungume Bakura yayi yana murna"karka  damu awaana" awaana na nufin d'an uwa._

_Cikin sauri ya nufi kasuwa ya siyo nama, tare da kayan amfani. Nan da nan Hajja ta hau hidimar bak'i, biskin gero da miyar kub'ewa tayi musu yasha manshanu gefe kuma soyyayar kaza ce. Ni kaina sai da nayi sha'awa. Hajja na  gamawa, ta had'a masa ya d'auka sai gidan Hajja._

_Kai tsaye gidan Hajja Faanah ya nufa, cikin nutsuwa ya yi salama. Daskarewa ya yi saboda mamaki, ba komai ya haddasa masa hakan ba face ganin Faanah. Durkushe take gaban d'an magen Hajja tana wasa da shi. Bai tab'a zato haka kyanta yake ba, kwata-kwata a hoto munninta ya hango. Gashinta ya rufe mata ido saboda yawansa da santsi, gyaran murya ya yi yai salama daga ciki Hajja ta amsa. Ya shiga yana murmushi ya sauke farantin hannunsa wanda aka jera kayan. Cikin murmushi Hajja ta dubeshi "sannu da k'ok'ari Hamza, hada hidima"?. Cikin murmushi ya sunkuyar da kai, mahaifin Faanah ya bishi da kallo yaron ya birgeshi sossai cikin ransa yana k'udirta wani lamari._

_Murmushi yayi ya fito zuwa tsakar gida, a hankali ya zauna yana fuskantar Faanah yana murmushi. Cikin barbanci ya ce"ba magana k'anwata?", da hannu ta nuna masa alamun bangane ba. Hamza yai murmushi a fili ya furta "kash! Tsutsa baki cin ragon goro", cikin tausayawa ya dinga kallonta. Fitowar Hajja yasa ya mik'e yana dubanta yace, "Hajja ina so mui magana da takwararki ban iya ba". Murmushi tayi "da sannu zaka iya Hamza rai dai" , murmushi yayi ya kad'a kai yayi wa Hajja salama ya wuce._

_Bakura noma yake sossai, Allah yasa masa albarka. Ubangidansa mutum ne mai saki masha Allah cikin ikon Allah, ya had'a shi da wata budurwa a wani aikin gona da ya fita yi mai suna Yakura. Yakura masifaffiyar yarinya ce ta bugawa a jarida, irin matan nan ne gansama-gansama masu suffar k'irar doki doguwa ce mai tsayi kakkaura. Bak'ace ba can ba tana da tsage guda biy-biyu a kumatunta wanda suka fito da fuskarta sossai hancinta mai tsayi sossai. Tana da yalwar gashi. Asalin mahaifanta 'yan garin Gamborun kukawa ne aiki ne ya kawo su garin Biu. Mahaifinta mutum ne mai mata biyu, da yara guda goma sha biyu. Yakura itace babba mahaifiyarta mafad'aciyyar mace ce. Sunanta Yagana, su biyu ne mata a wajanta ita da k'anwarta Yalfata. Sai maza akwai Alanguburo, Barma Hamza da kuma Muktar. Kishiyarta Yawuri yaranta duk mata ne, hakan ya haifar da k'anannun maganganu tsakanin zaman Babbar 'yarta itace Kundum yarinya mai hak'uri sossai, sai mai binta Bintu da Findu sai kuma Yazeyi da autarsu Yalta.Zaman gidan wani irin zamane na ishasshiyar mace hakan yasa mahaifiyar su Kundum bata da sakewa sossai asalinsu 'yan garin Askira ne .Kundum na aure a Gwaza Bintu a nan Biu Findu ce take Maiduguri Yazeyi Askira take sure sai auta Yalta dake karatu._

_Tunda Allah ya had'a Yakura da Bakura, suke wa juna. Yakura ta shiga ta fita ta hana zuciyarsa sukuni. Daga ita har mahaifiyarta, saboda bata son ya kub'uce mata. Dalili duk wanda yazo neman auranta yaji bata da mutunci guduwa yake, hakan yasa su kaiwa Bakura ruk'on talalla ya kasa koda motsi balle guduwa. Komai ya rarrumo to Yakura ce mutum ta farko, hatta da Hajja da Hamza ya tsaya da hidima da su hakan ya soma kawo nak'asu a karatun Hamza._

_Kwanci tashi kwannan su Faanah uku a garin Biu, zuwa lokacin sun yi wata irin shak'uwa da Hamza sossai, in basu ga juna ba kamar sa yi zazzab'i tun Hamza bai iya maganar kurame ba har ya koya.Faanah gidan su Hamza take yini suna hira abinda ya bashi mamaki har rubutu ta'iya in ya fad'a Hajja ta kanyi murnushi tace "nakasa bata hana bawa zama managarcin mutum"._

_Kwatsam ranar wata Asabar ana saura kwana hud'u su Faanah su koma Canada, tana gidan su Hamza suna hira suka samu bak'uncin Yakura da Yelta. Lamarin da ya haifar da rud'ani cikin zamantakewa............_
_Tunda sukai salama suka shigo Yakura ta kasa d'auke ido akan Fannah, zuciyarta na wani irin suya tsananin kishi ya kasheta. Bakura ya kasa tsaye sai nan da nan yake yi da su. Zama sukai suka gaishe da Hajja ta amsa da fara' a. Hamza kwata-kwata yak'i kallonsu ko d'aya Yakura bata birgeshi, sai da Bakura ya yi masa magana sannan ya juyo ya gaishe su. K' ur! Idanun Yalta a kan Hamza, zuciyarta ta shiga bugawa nan da nan so yai mata dabaibayi. Fuska a d'aure ya juyar da kai ya cigaba da yiwa Faanah hirarsu irin ta ma'abota kurumta sai dariya take wani lokacin tayi murmushi. Yakura ta nisa tace"Bakura dama kana da k'anwa?" Murmushi ya yi  yai mata bayanin Fannah a wajan su.Dai-dai lokacin Hajja ta basu waje, kamar jira take tana barin wajan ai kuwa Yalfata ta kwashe da wata shu'umar dariya"hhh! Nida durum kace bata ji?". A zuciye Hamza yayo kanta bai wata wata ba ya kwasheta da mari, cikin takaici ya nunata da yatsa zuciyarsa na zafi_.

_Bai an karaba yaji saukar mari a kuncinsa, cikin kad'uwa ya juya saboda ganin wanda ya mareshi abin mamaki Bakura ne. Ransa ya yi zafi ya dinga dubansa a wani irin yanayi kawai sai ya girgiza kai ya wuce. Hannun Fannah ya kama suka wuce zuwa gidan Kakarta. Tunda ya fita ya kasa magana, sai ajiyar zuciya yake. Faanah ta kama hannunsa ya zuba mata ido, sai ta girgiza kai shar hawaye ya zubo mata. Rikicewa yayi yana girgiza kansa bai taba ganin kukanta ba sai yau "shin me hakan yake nufi? Kodai Faanah najin abunda nake ji a raina?" Hannu yasa ya share mata hawayan suka nufi gidan Hajja da fara'arsu suka shiga. Hajja da mahaifiyar Faanah da mahaifinta na zaune suna fira, cikin murmushi suka zauna. Faanah nasan yiwa Hajja bayanin abinda ya faru ta kasa. Fahimtar hakan yasa Hamza yai mata bayani gudun zargi. A hargitse mahaifinta ya mike yana masifa" sun san kuwa yadda nakeson 'yata? Kurumta baisa ta zama wofintaciyya ba mutum ce mai cikakken yanci kamar kowa". Hajja ce ta dinga tausarsa haka ma Hamza bayan komai ya lafa Hamza ya dubi Hajja yace "Hajja wai haka aka haifi takwararki ko lallura ce?". Ta bud'e baki zatai magana sai gani nayi ta mik'e zumbur!. Ku biyo ni_

_Cikin murmushi Hajja ta dubeshi "sarkin tsoro naga randa zaka daina tsoron nan naka"dariya ya yi yana soka kai ta cigaba "yau dai zaka ji wacce ce Faanah?"..........._

_*WACCE CE FAANAH*_
_Kamar yadda ka sani ni na haifi mahaifin Faanah, shi kad'ai na haifa a salin mahaifinsa d'an Damaturu ne tsakanin Damaturu da Maiduguri tafiyar 177km ne ya taso cikin taskun 'yan uba su goma ne. Shi kad'aine waraki a cikinsu saboda mahaifiyarsa Bahaushiya ce 'yar Kano. Tsangwama da hantara babu wadda mahaifiyarsa bata gani ba, harta rasu sai tsangwama ta dawo kansa. Saboda Kanuri bayason auran wanda ba k'abilarsa ba sai rantsattsan rabo. Haka ya taso cikin gararin rayuwa, har girmansa Allah ya taimake shi mahaifinsa ya tsaya masa kan karatu. Allah ya had'amu da shi ne a wata ziyara da ya kai garin mu Gaidahm  gidan marayu cikin k'ank'anin lokaci mukai sabo dashi._

_Kasancewata marainiya bani da kowa kawai na taso ne na tsinci kaina a gidan marayu. Bayan dogon bincike aka bawa mahaifinsa aurena, zaman wata biyu mukai a Damaturu akai masa sauyin aiki zuwa Biu. Zamanmu a Damaturu zamane na hantara da hancini, dawowarmu Biu sai muka samu kwanciyar hankali a haka Allah ya bani juna biyu harna haifi d'a namji wanda yaci sunan Muhammad. Dangin mahaifinsa babu wanda yazo mana har ranar suna, kwanci tashi mahaifinsa ya soma sana'ar gwal nan da nan Allah ya bud'a masa ya zama shahararran mai kud'i. Lokaci zuwa lokaci muna zuwa ziyara gidan marayu da kuma Damaturu duk da bama samun wata tarbar kirki.Muhammad nada shekaru uku Kakansa ya rasu, mutuwar ta girgizamu dama shi kad'ai ne wanda ya rage mana. Bayan rasuwarsa sukai raban dukiyarsu kowa akabashi tasa suka watse. Kwanci tashi akasa Muhammad a makaranta kulawa yake samu sossai, harya gama makarantar primary ya shiga secondary. Yana jss two wata masifa ta samemu, barazana da yake samu daga abokan kasuwanci. Saboda ya tara dukiya da yawa duk garin Biu ansanshi, kwatsam wata ranar Lahdi da dare muna bacci aka hauro aka kashe shi. Lamarin daya girgizamu, sunyi bincike basu samu komai ba, saboda duk wata ajiya tasa tana banki wala kud'i wala kaddara._

_Haka muka sha kukanmu muka more, haka na cigaba da rainon d'ana na ingantashi da karatu da tarbiya har ya kammala makarantarsa. Na sama masa gurbi a makarantar kud'i nan yai karatunsa na shekaru shida na gaba da secondary daga nan ya samu admission a jami'ar Maiduguri bayan gama karatun sa na master yai aure, ya auyi Maryam 'yar a salin garin Maiduguri cikakkiyar Kanuri kyakkyawa gaba da baya. Zamansu shekara d'aya ya nemi gurbin k'aro karatu a k'asar Canada. Naso hanashi amma daya gayamun k'udirinsa saina hak'ura suka tafi. Shekarar su daya da tafiya aka haifi Fannah wadda taci sunana. Naji dad'in yimin takwara da akai sossai, daga can ya aiko abokinsa ya tafi dani akai suna na dawo. Sai da suka shekara uku sannan suka zo wajena lokacin Faanah ta girma, abinka da rainon turawa tayi girma sossai kamar 'yar shekara shida gata kyakkyawa. Abinda ya bani mamaki tunda suka zo banga tayi magana ba, tun ina kawaici har na furta. Cikin jimami sukai mun bayanin *KURMA CE* da farko hankalina ya tashi amma daga baya na fawwalawa ubangiji domin shiya hallice ta ya fimu santa._


_*Haka suka gama hutun su suka koma, tun ban iya hira da'ita ba harna koya nayi kewarta sossai. Bayan gama karatun mahaifinta Canada suka d'aukeshi aiki hakan ya tilasta musu zama a can. Zamowar Faanah Kurma baisa ta samu rashin kulawa daga iyayye ba hasalima tsananin sonta suke yi sossai, makaranta mai tsada suka sata abinka da kasasshen ketare sossai Malamai suke bata kulawa. Yanzu Faanah nada shekaru goma sha biyar tana matakin karshe a makarantar gaba da primary, ta iya rubutu sossai saidai bata ji kwata-kwata haka ubangiji ya hallici baiwarsa...........wannan shi ne tarihin Faanah._ 

_Ajiyar zuciya Hamza ya yi yace "kin san me Hajja?" "Saika fad'a Hamza". "Walahi banyi zaton haka aka haifi Faanah ba kin san akwai........_
 shi, ya dauko ya daga.Sun jima suna magana sannan ya katse ya soma bayani._

_"K'ananan yara tsakanin wata shida zuwa shekaru uku sukan yi fama da wani irin ciwon kunne da ake kira Otitis media, shi otitis media ciwo ne wanda yake ciwo a tsakiyar kunne._

_Ciwon kunnen yafi faruwa da damina kuma yana zuwa da zazzab'i wani lokaci mai tsanani,sai dai sau da dama bai cika zama abun damuwa ba._

_Akwai kuma wani ciwon kunnen da ake kiransa otitis external, wanda shi kuma yake shafar wajen kunne. Koda yake yara basu cika kamuwa da shi ba  kamar na farkon ba._

_Yawanci k'ananan yara suna fama da ciwon tsakiyar kunne, musamman k'ananan yara daga cikin wannan jerin:-_ _Yaran da aka haifa basu kai lokacin haihuwa ba.Akwai yaran da suke yawan jin sanyi sosai.Sannan akwai yara wad'anda basa son wari, kamar hayak'in taba da sauran su.Ko kuma yaran da ba’a basu nono ba.Da kuma yaran da aka baiwa abincin gwan gwani._

_Wasu k'wayoyin cuta suke kawo ciwon tsakiyar kunne.K'wayoyin cutar na tafiya daga bayan mak'ogoro yayin da Eustachian tube ta lalace,wannan ke kawo ciwon tsakiyar kunne.Shi yasa yara masu yawan jin sanyi ko masu fama da ciwon mak'ogoro ke kamuwa da ciwon kunne.Otitis external shi kuma yawanci yana faruwa saboda rashin tsabtar fatar jiki da k'wayar bacteria._
_Cikin murmushi Mahaifin Faanah ya dubeshi"shin ya alamomin ciwon suke Dr Hamza?". Dariya Hamza ya yi yace"haba Baana ban kai ga zama ba just one level fa". Gaba d'aya sukai dariya, banda Faanah da tai zuru tana kallon su, tausayinta ya cika Hamza ji yake tamkar ya bata kunnuwansa. Kad'a kai ya yi yaci gaba._

 _Alamun ciwon:-Ciwon cikin kunne (Otitis media), yawancin manyan yara suna fama da k'aik'ayin kunne da zafi.K'ananan yara basa iya Magana,amma zasu kasance da zazzab'i marar misali._

_Haka nan zasu kasa yin barci, su rik'a sosa kunnen su har yayi jinni, kuma suna kasa iya sauraron k'ara ko amo.Za’a iya samun fitar ruwa mai k'wayoyin cuta daga kunnuwan.Ciwon bayan kunne shima yana da zafi sosai, yana sa k'uraje sossai a bayan kunnuwa._

_Ana iya ba yara 'yan  k'asa da wata shida maganin kashe k'wayoyin cuta (Antibiotics).Shan maganin rage zafin ciwon.Yara suna jin sauk'i yayin da suka fara amfani da maganin kashe k'wayoyin cuta.A nan yana da muhimmanci ga Iyaye su kiayye umurnin likita har k'arshe.Shan Topical antibiotics da man shafawa suna maganin otitis external.Sake ganin likita na da amfani idan yaron yana da ciwon kunne ko yana amai sossai.Idan kuma yana da zazzab'i fiye da sa’a 48, da kumburi bayan kunne, idan yana barci sosai, kuraje a kunne, baya ji sossai ko gaba daya._

_Kunne yana d'aya daga cikin sassa masu muhimmanci sosai a jikin d'an Adam.Wanda ba kasafai ake gane muhimmancinsa ba, sai ya kamu da wata matsala._
_Kuma amfaninsa ba wai kawai a jin magana ya tsaya ba, a’a yakan kuma taimaka wajen sa dai-daito idan mutum ya mik'e tsaye ta yadda ba zai fadi kasa ba._

_Kunne na da b'angarori uku, na waje da tsakiya da kuma can ciki.Fatar kunne da k'ofar kunne ta waje su ne bangare na waje d'in.Amfanin wannan sashe shi ne tare iska da amo ya saita su zuwa cikin kunnen. Wannan b'angare bai cika samun ciwo sosai ba, sai dai akan iya yanke shi a hadari, ko kuma da abubuwa masu kaifi idan wata tarzoma ta tashi misali.Ita kuwa k'ofar kunne ana iya ganin dattin kunne a ciki a fitar ta wannan bangare.__B'angare na tsakiyar hade yake da mak'ogwaro ta yadda kwayoyin cuta daga makogwaron kan yi saurin shiga kunne, musamman ga yara tunda hanyar da ta had'asu gajeriya ce.Ruwa ma kan iya shiga wannan b'angare na kunne a yayin wanka ya hana mutum sakat._

_Daga can ciki kuma akwai wani b'angaren,inda dodon kunne wato cochlear (da kike tambaya akai) suke, da wasu kasusuwa kanana guda uku.Jijiyar da ke da alhakin sa mutum jin magana a jikin dodon kunnen ta ke.Wato ke nan dodon kunne shi ne ke da alhakin jin magana.Su kuma kasusuwan sukan taimaka wa jiki wajen daidaito._

_Abubuwa da dama kan taba lafiyar dodon kunne har a rasashi ta hanyar hujewa;abubuwan su ne kwayoyin cuta (kamar sankarau) ko wasu magunguna, na nasara ne (kamar gentamicin) ko na gargajiya, ko kuma a hud'a shi ta hanyar susa da abu mai tsini, ko kuma ta hanyar fad'awa ruwa da karfi, ko buguwa ta hadai,ko ta yawan shan kara fiye da kima, ko ma abin ya faru tun a ciki, a haifi mutum haka ba ya ji.Akan iya yin dashen wani dodon kunnen idan bukatar hakan ta taso._ _Idan ruwa ya  shiga kunne, misali kamar a lokutan wanka, za a iya sa tsinke mai auduga a goge.Idan bai fita ba a bari bayan kamar kwana biyu zai tsane da kansa.Sai idan ba a ji ya tsane da kansa ba ne ya kamata a je asibiti._ _Masu aiki a kamfanin da suke da injina masu  kara ko filin tashin jirgin sama, dole su rika toshe kunnensu a kullum, domin kiyaye lafiyar dodon kunne.Irin wannan kara ma takan iya fasa dodon kunne.Masu aiki a irin wad'annan wurare yana da kyau su rik'a zuwa wurin likitocin kunne a kalla sau d'aya a shekara don kula da lafiyar kunnensu.Hak'k'insu ne su nemi kamfanin ya samar musu abin rufe kunne da kuma likitoci domin kula da lafiyar kunnensu.A kasashen da suka ci gaba, idan babu irin wannan a kamfanin,ma’aikata za su iya kai kamfani k'ara kotu don a tabbatar an samu yanayin aiki wanda ba zai taba lafiya ba._
_Wad'annan su ne hanyoyin da za su iya sa a kamu da ciwon kunne, dama wasu hanyoyin daban-daban.Ga hanyoyin kariya daga ciwukan kunnen;-A mafi yawan lokuta ba sai an fitar da dattin kunne ba, dattin da kansa yake fita.Wato kunne shi ke wanke dattinsa da kansa.Yakan wanko shi ya turo shi k'ofa kunne.Za a ga dattin launin ruwan kasa a nad'e a jikin wani abu mai dank'o.Idan har ta kama sai an cire wannan abu mai danko, to kada a yi amfani da abu mai tsini.A sa irin abin goge kunnen nan mai auduga a bakin kunnen a fito da shi a hankali._

KARIYA

_Wanke hannuwanka da na yaro.Shayar da yara da nonon uwa.Dena ba yara abincin kwalba lokacin suna kwance.Daina amfani da kayan susa.Daina shan taba a d'akin da k'ananan yara suke.Yiwa yaro rigakafi da yana rage wannan ciwon.Yin allurar rigakafin mura mai zafi (Fluvaccine) kowacce shekara.A k'arshe, idan yaro ya kamu da ciwon kunne:Kada ayi amfani da auduga a kunnen,domin zata iya k'ara girman k'wayar cutar.Kada a diga maganin kashe k'wayoyin cuta a kunnuwan yara, zai iya kawo fashewar kunne.Kada a share kunne da auduga domin kauda dank'o kunne."_

_Gaba d'aya suka saki ajiyar zuciya, Hajja ta dinga murmushi tana jinjinawa Hamza. Haka ma Mahmmad, a ransa yana ji ina ma Hamza zai yarda ya zama yaron shi saboda yana da burin bud'e shaguna a garin Biu dan hab'aka garin. Kasa hak'ura yayi sai da ya furta sossai Hajja taji dad'in k'udin d'anta. Hamza kuwa murmushi ya yi yace su bashi lokaci ya yi shawara da Bakura da Hajjansu. Sun amince da batunsa saboda yana da na gaba dashi. To nima bari in je in huta kafin in d'ora nagaji da yawa Lo
_Washegari Hamza bai yi k'asa a guiwa ba, ya sanar da Hajja k'udirinsa. Hajja ta nuna masa rashin amincewarta ta nuna masa karatunsa yafi komai muhimmanci a gareshi. Bai jinkirta ba ya sanarwa da mahaifin Faanah shima baiga laifinsa ba saboda yasan muhimmancin karatun._

_Kwanci tashi kwanaki na shud'ewa, harzuwa lokacin babu jituwa tsakanin Bakura da Hamza. Hamza da Faanah sunyi wata irin shak'uwa sosai. Ranar da mahaifanta suka saka zasu koma Canada, Faanah ta dinga ihu tana kuka kan bazata bisu ba. Hankalinsu ya tashi sossai, a rayuwarsu basasan b'acin ranta saboda yarinya ce mara son hayaniyya duk da kassncewarta Kurma. Tilas suka hak'ura suka barwa Hajja ita da sharad'in zata koma in hutun Hamza ya k'are ya koma makaranta. Haka suka rabu suna ta jimamin rabuwa da juna.

_Ashe tafiyar ajali ce a ranar jirginsu ya samu accident (had'ari), babu wanda ya rasu a cikin su. Lokacin da labari ya samu Hajja fad'uwa tayi sumammiya lamarin daya haifar mata da cutar shanyewar b'arin jiki. Al'ammarin daya d'aga hankalin Hamza da Hajja Falmata Allah sarki Faanah kuka ma gagararta ya yi sai zubar hawaye.

_Kwananta goma a asibiti babu abinda take iya yi, kwata-kwata jikinta baya motsi.Hamza ya shiga faffutukar neman kud'in magani, abun yaci tura. Aikin yi ya gaggara kasancewar damuna tayi nisa, hakan yasa ya shiga mawuyacin hali saboda tausayin Faanah. Cikin ikon Allah ya samu aikin kwaso wani barkono daga wata gona zuwa gidan maigari. Yana kammalawa aka biyashi naira dubu goma, ya juya kud'in ya jinjina a ransa yana tunanin ko zasu isheshi hidimar kulawa da Hajja.Kwana uku yana tunanin lamarin, ya dauki kud'in ya dank'awa likita dan bata kulawar data dace. A haka yaci gaba da neman wani aikin, Hajja Falmata ita take kawo abinci kullum yayin da Faanah da Hamza ke jinya.Ranar kwana na sha hud'u ta amsa kiran mahallicinta. Haka rayuwar take (KULLU NAFSEEN ZA'IKATTUL MAUT),haka aka tattara Hajja zuwa gida akai mata sallah aka sadata da makwancinta na gaskiya. Ubangiji kasa mui kyakkyawan k'arshe amin.

Kacokan Hamza ya tattaro kayan Faanah zuwa gidansu, babu uwa babu uba babu kaka. Rayuwa ta yi mata k'unci Hamza da Hakka ne kad'ai take kallo taji dad'i a ranta. Hutu ya k'are Hamza babu kud'in komawa makaranta, duk yadda yaso abun ya gaggara ya tirza ya tirza abu ya gaggara, Hajja ce ta tunkari Bakura da batun, atabau yace bazai bayar ba shi yana so ne ya k'arasa had'a kud'insa ya siyi sissin gwal wanda zai kaiwa dangin Yakura na neman auranta. Sossai Hajja taji haushin abinda Bakura ya yi, amma bata nuna masa ba. Lamarin ya sha kansu sossai, Hamza ya shiga damuwa abokansa duk sun koma makaranta banda shi.
Ranar wata Asabar suna zaune jigum, Hamza yana yiwa Hajja bayanin aikin daya samu na gonar mak'ocinsu mahaifin su Alangubro. Faanah ce ta fito ta ratso tsakar gidan tana murmushi, wani abun hannu mai kauri ta ciro a hannunta guda hud'u ne ta bashi guda biyu, batai magana ba ta tamke fuska ta koma d'akin Hajja yasan ni sarai, koda ya kirata bazata juyoba. Cikin murmushi ya dubi Hajja yace"Hajja 'yarki rigimammiya ce, kwana uku kennan ina fama da'ita wai saina saida abun hannunta na koma makaranta. Hajja bawai siyarwa ne bana son yi ba, asalin abun hannun na mahaifiyarta ne kinga a yanzu Faanah bata da komai data samu daga mahaifanta inba awarwaron nan ba sai gidan Hajja." Ajiyar zuciya ta yi "lallai kayi gaskiya Hamza dad'ina da kai hankali amma tunda ta dage ka karb'a saika siyar da biyun ka ajiyemata biyun. Intaga babu su a hannunta gaba ai banga abunda zata ce a siyar ba".
"To! Shikenan Hajja", da haka suka kashe maganar. Cikin satin aka kai abun hannun kasuwa, abinda ya bashi mamaki dubu d'ari da hamsin aka siyi kowane d'aya, hakan yasa ya saida d'aya ya dawo da d'ayan ya karb'i biyun ya had'a ya ajiyemata. Dubu hamsin ya karb'a ya bawa Hajja dubu hamsin taimusu siyyayar kayan masarufi na dubu ashirin, dubu ashirin yace asiyawa Faanah kayan dangin turare da lafayya da mindil ai kuwa tayi murna sossai. Dubu hamsin ya ajiyeta zai yi noman gyad'a da barkono. A satin ya koma makaranta.

Tun komawarsa makaranta ya kasa sukuni, kwata-kwata tunanin Faanah ya hanashi walwala. Da farko ya d'auka sabo ne, turken wawa daga baya sai salon ya sauya. Lokuta da dama muryarta har gizo take yi masa a kunnuwansa. Lamarin ya d'aga masa hankali ya kan yawar tambayar kansa "ina ni ina soyyaya da kurma?" Amsar da take bashi wuyar samu a koda yaushe. Ba lallurarta yake gudu ba, yadda Hajja zata karb'i lamarin, zahirin gaskiya da farko tausayinta yake ji daga baya ya gama amincewa zuciyarsa san Faanah yake.Kwanci tashi suka cinye samister d'aya, suna shirin fara jarrabawa kullum adu'arsa ubangiji yasa ya haye matakin karatunsa.
Faanah na samun kulawa dai-dai gwargwado wajan Hajja,tun bayar tafiyar Hamza ta fahimci kad'aici ya yi wa Faanah yawa, ana haka aka bud'e wajan koyon sak'ar hannu kusa da su. Batai wani jinkiri ba ta yankar mata form ta soma zuwa.

Tana jin dad'in zuwa sossai, nan da nan ta maida hankali akai ta soma yin safa da abun goge gumi.

Tun bayan komawar su Yakura gida, Yelfata ta kasa nutsuwa. Kwata-kwata zuciyarta na wajan Hamza ya burgeta matuk'a amma data tuna Faanah sai gabanta ya yanke ya fad'i ta tabbatar akwai wata alak'a irin ta zuciya tsakaninsu. Saboda yadda taga yana nuna mata kulawa a zahiri, da kuma yadda ya taso mata tamkar mayunwacin zakin da ya shekara be ci ba.
Zaune take tayi nisa cikin tunanin, Yakura ta jima a tsaye a kanta bata san tana kanta ba har saida ta d'an tab'ota. A jiyar zuciya ta saki tana dubanta"lafiya Yalfata, meya sameki ?"Hmmm! Babu komai Yakura". "Ke! Dakata ni zaki b'oyewa damuwarki?", tayi jigum tana tunani ta nisa tace "Yakura inason Hamza". Cikin tashin hankali ta zaro ido "awaana Bakura? ('Dan uwan Bakura). Kai ta d'aga mata tana jinjinawa. Yakura ta jinjina, ta sake jinjinawa taja fasali ta dubeta.Download Complete Here

Saturday, 6 October 2018

Video: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 74

October 06, 2018 0

Alawiyya ta yi wani yunkuri abin yabawa. Wani malamin boko, malam Danbala ya fara tabka tabara. Kawun Dan Tani wato Kuma Manu ya dau zafi. Adama da kyauta dillaliya sun warota


Hausa Novel: Amal ( By Zainab Naseer Sarki )

October 06, 2018 0


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL 
      NA
Zainab Naseer Sarki
  (Zeenaseer😘)

1-5

Amal! Amal!!
Hjy ladi take faman kwala mata kira kamar Wanda makoshinta zai fito waje.hakanne hakan ne yasanya Amal rawar jiki,da murya mai rawa tace,ganinan hajiya.tsoki tana sannan ta koma saman kujera ta zauna,tana faman mita.yarinya sai shegen nawa,saikace wacce zata gasan sarauniyar kyau,karasa ubanme take,acikin daki,wani tsaka taja,sannan takuma bude murya ta a fusace.wai ubanme kikiye cikin dakinnan,wlh kika batamin lokaci jikinkine zai gaya miki,sai shegiyar nawa kika iya,cikin hanxari tafito daga dakin tana daura dankwali.cikin zuciyarta tana fadin,ko minti goma mutun beyiba amma ake faman yimasa fada kamar za'a cinyeshi.
Zuwa tayi ta durkusa agaban ta,kanta akasa,cinkin rawar murya tace hjy gani Dan girman Alla.....,Bata karasaba ta kwasheta da wani wawan mari,daya sata kifawa ba shiri ta dafe kuncinta tana hawaye.
  Ubanme zaki gayamin shegiya mekama da aljannu,wallahi saina hanaki yin wankan gaba dayama,kin mai danima sa'ar wasanki,kin barni tun daxu anan ina faman jiranki,kuma kinsan sarai fita zanyi.
Cikin muryar kuka tace kiyi hakuri wallahi bansan fit......,Rufemun baki munafuka,inma kinsani fadamin zakiyi,wallahi kika cikani saina fasa miki baki,cewar hjy tana zaro Ido waje.
Ki bude kunnuwanki dakyau kijini,zanyi bako Dan gidan hajiya bilki zaizo daga London, kuma anan gidan zai zauna,Dan tayi tafiya zuwa Dubai. Girki zakiyi mai,kuma ki hadami drinks, sannan ki huce ki gyaramai wannan dakin nawajan garden. Kina jina ko kuwa.cikin rawar murya tace eh.yauwa saura kuma kimin hauka wallahi saina karyaki.
Cikin muryar kuka tace hjy ammafa yau kusan satina biyu banje islamiyaba kum.....,kuma me,kina nufi bazakiyi abunda nasakiba kenan.lallai Amal huyanki ya isa yanka,wallahi saina hadaki da ubanki,inni ban isa dakeba,shi ya isa dake.cikin kuka ta rike kafafunta tana kuka,wallahi zanyi hjy Dan Allh karki sanar masa,zanyi.mikewa tayi tare da hankade ta tafada sanman kafet,en dakin tana kuka.karma kiyi,gyalenta ta yafa,tareda rataye jakarta,tadau key din matarta ta fice daga falon.
Wani irin kukane mai karfi ya kwace mata,wannan wani irin ukubane ni Amal nake ciki,yaushene zansamu gata irinna kowane da,Allah na rukeka kasamamin mafita ya ubangiji,hawayene me zafi taci gaba da bin kuncinta.
Abun bakin cikinta shine ace itada gidan ubanta amma yn aeki sunfita samun hutu.kukan tacigaba dayi bame lallashinta harna wani Dan lokaci.
Hanne me aikici ta shigo Wanda shekarunta baxe dare na Amal enba.haba Amal kuka kuma,Dan Allh kiyi hakuri,nasan koda baki fadaba hjy ce,amma inda sabo kin saba,so kike kijama kanki wani ciwon ko Amal? Dan Allh kibar kuka kinji,badamin yanxu me zakiyi.
Hanne kinsan yau kusan satina biyu rabuna da islamiyah,kuma hadda zanyi amma shine hjy saboda tsabar mugunta tabani wani uban aeki,Wanda bawani nataba za aemawa,kawai dan gidan kawarta.hmmmm to shikenan naji yanxu de babu abundant zanyi taso muje muyi tare,dn Allh kibar kuka,baranaje na shanya kayan nan,saina dawo kinji tashi.Ahnkali ta taimaka mata ramike tabar falon.
Komai tare sukayi da hanne Har gyaran dakin,sai wajajan 4:00pm sannan suka kammala.
Saman dinning suka jere abincan da drinks en.sanna ko wance tayi dakinta da tsaftace jikinta.
     Misalin karfe 5:00pm daidai jirgin so Annur ya sauka a airport en jigawa.bayan en mintina da saukarsa fasinjoji suka fara saukowa.
Ahankali yake takowa daga steps en jigin zuwa kasa,iska mai ddi tana kadawa,fuskarshi dauke da murmushi,fone inshine yayi kara,cikin nutsuwa ya sanya hannun shi cikin aljihunsa,da amsa kiran.murmushi yayi lokacin dayaga sunan me kirannashi.
Hello ummina abunda ya fada tare da kara wayartashi a kunne.daga dayan bangaran ta amsa, Son kun sauka lfy.lfy qlau Ummi.yauwa ga kawatana hjy ladi tun daxu take jiranka,a gidan ta zaka sauka nasan zata kulamun dakai sosai kaji son,cikin sanyi jiki yace ohk.be jira cewartaba ya katse wayar,Dan harga Allah ya tsani wadannan frnds en na umminshi Dan de bayanca zaiyi.
Hajiya ladi dake zaune akujerun gurin,lkc lkc tana kallon agogon hannunta,da tun around 4:30pm take agurin,waya dake rike a hannunta tana kallon pic en Annur da hjy Bilki ta turo mata.
Daga kan da zatayi ta hangoshi yana tahowa fuskarshi ba annurin dariya.baki bude take kallon sa,da ganinshi a zahiri.
Kyakyawan namiji dogo,me bakin suma da tsayi,yr madedeciyar fuska mai dauke da manyan idanu,a lumshe kamar namejin bacci,dagon hanci,da karamin baki,duk enda ake Neman namiji cikakke da yahada komai,kwarjini,ilmi,kudi,hankali,kasaita,Annur ya hada.
Gabanshi tasha tare da washemai baki,umm ..ammm Annur ko?kai kawai ya gyadamata tare da yimata Kallan mamaki,gaba yayi tareda jan trolley ensa,batare da yakuma magana ba,idonta ta kulle hadeda hade hanna yanta a kirji,son Annur na da da,shiga zuciyar ta,ta furta dulema alhaji kabar duniya Dan na samu cikar burina.
    
        Dis page goes to my best grp ❤BEST FRIENDS❤tnkuuu for d Lov nd care.
  
       Written by zeenaseer😘
[12/29, 10:34 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
          🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
      NA
Zainab Naseer Sarki
    (Zeenaseer😘)

5&10

Misalin karfe 5:19mp,
Suka isa kobar gidan Alhaji Aliyu Dutse,horn biyu me gadi yabude gate en gidan,hancin motar ta tura zuwa cikin gidan,a parking space tayi park en motar.a hankali tabude side enta na driver,tafito,A hankali ta nufi side en da yake axaune,kafin ta budemai ya futa a hankali,sannan ya nufi Boot da fito da kayan sa.sanna ya tsaya yana jiran ta nuna masa masaukin sa,cikin kararraya takaraso tana kissa,yauwa muje mana ko,nabarka kanata faman wahala,ko kallanta beyiba yaci gaba da danna wayarsa,saida ta kuma maimaitawa sannan ya nuna mata hanya.tana tafiya tana rangwada,shikuwa kota kantama bayayi,har dakin ta rakashi,sanna ta bude masa,kanshin turaran hutan da sanyin AC ne ya daki hancinsa,ahankali ya lumshe idanunsa Dan turaran yayi masa ddi.da sallama ya shiga dakin bakin gado ya anje trolley ensa,sannan ya juwa ya fuskanceta cikin sanyin murya yace nagodeee!.lumshe Ido tayi sabo da ddin muryarsa tare da rufe idanu.juyawa tayi tana rangwada harta fice,murmushi yayi danshi mamakima take  bashi,babba da ita amma take abun yara.hadawa yayi kan gadon tareda rufe idanun sa,ya bude ahankali ya saukeshi akan silin dakin.mikewa yayi ahankali yanufi toilet dan watsa ruwa.ya dade a toilet en Dan ruwan yayi masa ddi,sosai ya jima kafin ya fito ya sanya jallabiyan shi.
Masallaci yanufa danyin sallah magrib.
Bayan hjy ladi tagama tabaro dakin Annur, daki tanufa danyin wanka,bayan ta fito daga toilet zama tayi ta tsara kwalliyan ta,kamar wata budurwa,English wears ta sanya sannan matsatsato,tafbas tayi kyau.hjy dadi farace tas amma akwai Karin mai,tanada jiki,amma ko kadan bata da kyau,farinne kawai ya ceceta.
Bayan ta gama shirinta tamike cikin takunta na kasaita.dakin Annur tanufa tana rangwada.knocking tayi sau biyu sanna yabada iznin shiga,cikin sallama tashiga tana,ta huce bakin gado,tazauna kusa da kansa,a fusace ya miki yana kallan ta,meye hakane baki da hankaline,ko ke ba matar aure bacene,zakina shigewa mutumin daba muharraminkiba,pls kibar dakinnan karki batamin rai pls.cikin sanyin jiki tamike tanufi kofa,sannan ta juyo cike da kissa,dama cewa zanyi dakai abincinka na jiranaka.tana gama fadin haka ta turo masa kofar.tsaki yaja yana jin haushi irinna wannan ballagaxar mata.mikewa yayi badan yana soba,saboda yinwar dayake ji.
A dinning en ya sameta a zaune kujera yaja can nesa da ita ya zauna,yana danna wayarsa.kallonsa taci gaba dayi kamar mayya.
Amal! Amal!!
Amal dake zaune kan abun sallah tamike da hanzari tanufi kofar fita,a dinning ta sameta tare da bakwanta,cike da harara ta kalleta,kin tsayawa mutane,baki iya gaisuwaba,batare da ta kalleshi ta gaidashi,gabanshine ya buga lokacin dayaji murya mai ddi da sanyi,yana san dagowa ya kalli me wannan muryar amma yana ganin kamar ya zubda girmansa.
Dalllacan kizo kiyi serving en mutane suna jin yinwa,batace mata komai ba tafara zuba musu abincin.white rice ce,da stew tasha kaji,ta zuba masa fruit salad,da mango juice, sannan ta turamai gaban sa.tunda aka bude abincin kanshi ya cikamai hancinsa,burinshi kawai yafara ci yaji tests en abakinsa.
Jellof en taliya da tasha vegetable da kifi,ta zubama hajiya.sannan ta juya tanufi dakin ta.
Tafdi Jan!,abunda ya fito kenan daga bakin Amal,wato matarnan neman maxa kuma ta koma kenan,kina da auranki kizauna kina cin abinci da wani katan gardi,cikin irin wannan shiga,Allh ya kyauta.
Saida ya dauki kusan mintina goma kafin ya jawo abincin yafara ci,cikin nutsuwa,hajiya ladi data anje spoon enta,tana kallan Annur cike da so da kauna,komai nashi burgeta yakeyi,Allh ya bani wannan yaro,abunda take ta faman nanantawa cikin zuciyarta.shikuwa da besan tana yibama abincinsa kawai yakeci,cikeda jin ddin shi,yayi mai ddi sosai kamar Karya kare.sosai yadau lokaci kafin ya gama cin abincin,sannan ya shanye fruit salad en nasa,mikewa yyi,sannan ya nufi hanyar dakin sa.
Binshi kawai take da kallo kafin ta cemai saida safe.ko takanta be buba ya hucewar sa.naunauyar ajiyar zuciya ta sauke,sannan itama ta mike ta nufi part enta.

Sunday mrng 4:56am
           ******
Lokacinne Annur ya farka daga bacci Dan fita masallaci,Sauri yaketa faman yi Dan yamakara sosai.sannan ya fito.

Adaidai lokacinne Amal ta farka Dan gabatar da sallanta.Dan itama ta makara sosai.bayan ta idar da sallah ne,tadauko Alqurni Dan gabatar da tulawanta.Dama taruga da tasaba a kowace safiya.saida gari yafara aske sannna ta mike dan gabatar da breakfast.
A kitchen ta tarda hanne,wadda ta taho ragema Amal en aeki Dan tasan sarai itace meyin girki kowace rana.bayan sun gaisane,hanne tace wlh Dama yanxu nake shirin zuwa na tambayeki abunda xa'a Dora,murmushi tayi,hmmmm hanne kenan ae koma meye kawai ki dafa.toh sikenan bara muyi kunun gyada da fankaso kawai.shikenan ba,Amal tace barana kwaba fanken,ke saiki hada kunun,yauwa,suna hira suna aekin Dan dannan suka gama,kai dinning suka jera sannna suka huce Dan hutawa.
Sanye take cikin duguwan rigan atamfa,ammata kwalliyan White nd  green tayi mata kyau sosai.kai tsaye dakin Annur ta nufa.
Daidai lokacin yake fitowa daga wanka daure da towel a kugunsa,da wani a hannun sa yana goge kansa.karar bude kofar dakinne ya sashi dago da kansa wanda sukayi ido hudu da hajiya ladi.
Wani dogon tsaki yaje,wake wata irin matace wlh dolena nabar gidannan nibansan me yasa ummina ta hadani dakeba,taya zakina behaviour enki kamar na marasa ilimine,gaskiya banasan irin wannan,pls leave cikin muryar tsawa yake mgnar saboda ta fusatashi.
Murmushi tayi na en duniya,Annur kenan!,dama xuwanayi nagayama abi.......enough pls,kullum abinci to naji na gode,kuma bana bukatar kikuma shigo part ena pls.ya juya ya koma tailor cikin haushi.

MUJE ZUWA😜😜

Dis page goes to u nemcy Allh baki lfy ameen.

Written by zeenaseer😘

  08105857631
[12/29, 10:34 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
          🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
   NA
 Zainab Naseer Sarki
    (Zeenaseer😘)


Download Complete Here