Thursday, 22 November 2018

YA SAYYADI YA YI LALATA DA DALIBARSA A KANO


YA SAYYADI YA YI LALATA DA DALIBARSA A KANO

Daga Ibrahim Rabiu Kurna

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta yi holin wani Ya Sayyadi wanda wasu iyaye suka dauka don ya karantar da 'ya'yansu su 7 karatun Alqur’ani a gida amma ya yi amfani da wannan damar ya haikewa 'yar karamar su mai shekara 8  a cikin gidan.

Ya Sayyadin mazaunin unguwar Dakata, yana da aure ya ce yarinyar ce take matsowa kusa da shi tace masa za ta yi rubutu sai ya daga ta daga nan dai sai shaidan ya rinjaye shi har ya biya bukatarsa da ita.

Ya amsa laifinsa, inda yace kaddara ce Allah ya kawo masa hakan kuma ba ta taba faruwa akansa ba sai a wannan lokaci, ya nuna nadamar sa da yin da na sani akan abinda ya aikata na haikewa karamar yarinya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majia, ya ja hankalin iyaye da su lura tare da sanin irin malaman da za su dinga dauka domin koyar da 'ya'yan su karatu.

No comments:

Post a Comment