Monday, 5 November 2018

ME YA SA BA ZA MU YI WA MASOYA BUHARI UZURI BA?


ME YA SA BA ZA MU YI WA MASOYA BUHARI UZURI BA?

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

1. ALI NUHU

Miliyoyin masu kallon fina-finan Hausa sun yarda sun amince babu tauraro a kafatanin Kannywood kamar Ali Nuhu Mohammed  Shekara da shekara kusan duk wani shahararren fim din Hausa da ya yi kasuwa ya samu karbuwa a wajen 'yan kallo Ali Nuhu ne a ciki. Su kansu masu shirya fina-finan sun camfa fim idan ba shi ba ya kasuwa.

Tun da aka nada shi Sarkin Kannywood har yanzu shine akan gadon Sarautar an rasa madadinsa. Da dukkan alamu sarautar za ta zama tamkar ta Sarakunan Gargajiya da sai dai ko ya yi murabus ko kuma idan ya mutu a nada wani. Don haka dole ka yi musu uzuri idan suka ce babu sama da shi a harkar FIM.

An musu uzuri saboda an kasa samun dan fim da ya cimma Nasarorin da ya ke da su.

2. RARARA

Tun da Dauda Kahutu Rarara ya fara wakar siyasa ya zama ya yi matsanancin tasirin da ba inda wakarsa ba ta shiga. Kowane dan siyasa burinsa ace Rarara ne ya wake shi. Ya zama sanadiyyar girgiza miliyoyin matasa wajen sauya gwamnati. Zuwa yanzu babu wani mawakin siyasa da za ka ji ana Kace-nace akansa kamar Rarara.

 Masoyansa na kallonsa a matsayin babu mawakin da ya kai shi iya zazzago baituka cikin hikima da salo masu tarin yawa ba tare da gazawa ba. A cewar su ya fi kowane mawakin siyasa suna da daukaka a yanzu.
An Musu uzuri saboda babu mawakin siyasa da ya taka matsayin da ya taka.

3. MUHAMMADU BUHARI

A tarihin siyasar Najeriya babu wani dan siyasa da TALAKA ya nuna zunzurutun so da kauna kamar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Talakawa sun yi kone-kone gami da hargitsa Najeriya saboda zargin an murde masa zabe. Talakawa sun tara masa kudi don ya zama shugaban su.

Talakawa sun mutu saboda murnar ya ci zabe. Talakawa sun sha ruwan kwata, sun zuba ruwa a kasa sun sha, sun yi tafiyar dubban kilomita a kafa saboda da murna. Shine Malaman Addini suka hau Mumbarin wa'azi, Limamai suka hau Mumbarin Juma'a suna fadakar da Talakawa su zabe shi. Sun bugi kirji sun ce babu kamarsa a tsananin farin jini da tasiri a zuciyar Talakawa a yanzu.

Amma an ki yi musu uzuri duk da an kasa kawo wanda ya kai shi.
No comments:

Post a Comment