Thursday, 29 November 2018

Hausa Novel: K'ARSHEN WAHALA ( By Aishat A Muh'd)


🍀🍀☘☘🍀🍀
   *K'ARSHEN WAHALA*🍀🍀☘☘🍀🍀
            *NA*

     *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘

*GODIYA*
_Godiya ga Allah {SWA} da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin nawa tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabi Muhammad {SAW}_.....


  *JAN HANKALI*
 _Wannan littafin banyi shi don wani ba ko wata nayi shine don fad'akarwa,nishad'antar wa don hka a d'auki abu mai amfani a bar mara amfani abin da yake kuskure Allah ya yafe min,Allah yabamu ikon aikata dai dai a rayuwar mu ameeen_......

*ZUWA GA MASOYA NA*
_godiya mai yawa a gare ku masoya na,nima ina kaunar ku_.


*BAZAN MANTA DA KE  BA*
_my cwt Sadeey  S Adam {saNaz Deeyah} da irin k'warin gwiwar da kike bani da soyayyar da kike nuna min don *Adalilin son* da kike nuna min na kai hka Allah ya bar mu tare_.......


*~pg 1~*


   Yanayin unguwar irin unguwar masu hannu da shuni ce gwamna road a garin kd,family d'in gdn gaba d'aya suna xaune a k'ayataccen falon su hira sosae suke da kagan su kasan happy family ne  ....

   Alhaji sa'eed haruna kenan da matar shi hajia maimuna sai yaran su safah itace babba sai nauwarah da k'aramin su saleem,su kadai Allah ya basu don sun ma fitar da ran sake haihuwa tun da saleem ya kai 7yr's da haihuwa, suna matuk'ar kaunar 'ya'yan su sosae ana cikin hira caraf nauwarah tayi magana cikin shagwaba take cewa

    " _Abba gaskia ina son idan na kammala secondary schl malaysia nake son ka sama min university_"

Dariya abban yayi irin ta manya sannan yace
    " _nauwarah 'yar gidan Abba kada Ki damu Insha Allah xan cika miki wannan burin ke dai Allah yasa muna raye ki kwantar da hankali ki_"

Cikin tsananin murna tace
  " _Ameeen my abba na_"

Har ta bud'e baki  xata sake magana safah ta watsa mata harara kamar idon ta ya fad'o tace

  " _tabbb Lallai yarinyar ae yanda nayi karatu a 9ja ke ma hka xakayi ba inda xaki je_"

 Turo baki tayi cike da shagwaba tace " _uhm kaji aunty safah da wani xance kuma bayan ynx agaban Ki abba ya amince min koh abb?_"

  " _k'warai da gaske nauwarah ta haske mai kyau hasken idaniya ta da ixinin Allah xaki je ke dai ki dage da karatu kmr yanda na san ki_"

Wani tsalle ta buga tana ihun murna yayin da safah ta xumburi baki cike da haushi tace

  " _dallah malama kin dame mu da ihu idan baki shiru ba ynx na tashi na bubbuge bakin ki_"

Murgud'a mata d'an k'aramin bakin ta tayi cike da tsiwa tace

  " _kaji mu da aunty safah nan ina ruwan ki da ihu ba Naga dai murna nake_"

Axuciye safah ta tashi tayo kanta aikuwa da gudu ta b'uya a bayan ammin ta tana mata gwalo abba da saleem da ammi dariya kawai suke yi musu hannu tasa xata fisgo ta da sauri ammi ta tare tana cewa

 " _a'a safah yi hak'uri ki kyale ta kinsan yarinya ce kuma naga ae murna take_"

 " _amma dai ammi Kina kallo gwalo take yi min_"

Da sauri ammi ta juya bayan ta ae kuwa taga nauwarah gwalo take mata cikin fad'a ammi tace

  " _bana son hka nauwarah baki ga yayar Ki bace ji nake d'axu kika gama bibbige min saleem don ya tab'a miki phone d'in ki_"

" _tohh ammi na dai na yi mata_"
Ta fad'a kamar xata fashe da kuka murmishin mugun ta safah ta saki tare da cewa

  " _yarinya xaki xo ki same ni ne_"
Idon ammi ta faka ta Murgud'a mata baki yanda take Murgud'a bakin da ka gani kasan ta riga ta saba da hkan....


Ko _10 mints_ ba'a yi ba na hango nauwarah kusa da safah tana wani marairaice fuska tare da langab'e kai alamar tana son wani abu safah tana kallon ta ta gefen ido kamar xata tuntsire da dariya hka take ji dakyar ta iya  danne dariyar bata kula ta ba ta Kalli inda saleem yake tace

" _saleem dauko min maltina a frige mai sauk'in sanyi_"

Ae Kafin ta rufe bakin ta da gudu nauwarah ta nufi frige ta d'auko mata maltina ta Mik'o mata hararar ta safah tayi tare da cewa

  " _na ambaci sunan ki ne ae Naga saleem na aika_"
Murgud'a mata baki tayi cikin k'uluwa safah tace " _au  Murgud'a min baki kike_"

Da sauri nauwarah ta dafe bakin ta cikin marairaicewa tace
 " _hba aunty safah na mance ne I'm so sorry baxan k'ara ba ki karb'a kisha Kinsan baxan ji dad'i ba Idan baki karb'a ba plsss_"

Gaba d'aya falon aka kyalkyale da dariya ita kuma sai wani lalangab'e kai take da yake safah tana masifar son kanwar ta bata son abin da xai b'ata mata rai yasa ta karb'a ae kuwa ta rungume ta tana dariya ba wanda bai yi dariya ba a wajen.....

Tana shan maltina nauwarah cikin K'aramar murya tace " _Aunty safah yaushe xaki kaimu shopping ne gaskia kayan kwalliya na sun kusa k'are wa_"
Harara ta xabga mata kafin tace

 " _baxa ajeba sai ki nemi driver ya kai ki_"

" _Kaiiii aunty baxa ki kai ni ba don Allah ki taimaka plsss_"

Abba ne yace " _aunty safah ayi hak'uri akai ta mana_"

Hannu tasa ta dungure mata gaba d'aya aka tuntsire da dariya kafin tace " _kinci darajar abba yarinya_"

Cike da d'oki da murna tace" _xaki kai ni my cwt sister?_"

  " _xan kai Ki Insha Allah gobe 'yar cwt k'anwata_"

Murmishi tayi har dimple d'in ta ya lotsa tayi kissing d'in ta a kumatu tare da fad'in
  " _thank you so much my aunty safah_"

Saleem yace " _har dani xa'a je koh aunty safah?_"
Harara nauwarah ta xabga mishi tare da cewa " _baxa'a da kai ba yaro_"

B'ata rai yayi tare da cunkushe fuska kamar xai fashe da kuka da sauri ammi tace " _kada ma kayi kuka dole aje da kai_"

Xumbura baki nauwarah tayi tare da tashi ta nufi bedroom.......
    *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*🍀🍀☘☘🍀🍀
            *NA*

    *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘

*~pg 2~*  *WANE NE ALHAJI SA'EED HARUNA???*


 'Dan asalin garin kaduna ne a wata unguwa tudun wada anan mahaifan sa suke mahaifin sa Baffah haruna yana da rufin asirin shi dai dai gwargwado da matan sa 2 inna zainab ita ce babba tana da yara 2 sa'eed da mace safiyya sai inna larai d'an ta d'aya sunan shi salisu da yake Allah bai bashi yawan xuri'a ba......


  Baffah haruna yana matuk'ar kokari wajen kyautata wa iyalan shi da bawa yaran shi tarbiyya ta k'warai sai dai kwata kwata ba'a xaman Lfy a tsakanin matan na shi babu jituwa Ko Kad'an....

  Inna zainab mace ce mai hak'uri da kau da kai akan komai yayin da inna larai bata da hak'uri ko Kad'an saboda tana ganin baffah haruna ya fisan su zainab da yaran ta alhalin yana iyakar kok'ari wajen kwatan ta adalci a tsakanin matan shi da 'ya'yan sa.

   Axahirin gaskia yafi k'aunar zainab da yaran ta saboda sun fi mishi biyayya musamman sa'eed yana matuk'ar kaunar shi yaro ne mai hankali da nutsuwa bai dauki duniya da xafi ba shi yasa uban yake son shi sa6anin salisu da ya dauko halayar mahaifiyar shi akwai shi da mugun hassada da kyashin wani yayi abu shi bai yi ba baffah haruna yayi fad'an yayi nasihar duk a banxa don hka kawai ya kyale shi yana mishi addu'ar Allah ya shirya shi....         *******
  Bayan sa'eed ya kammala schl ya samu aiki a wani company albarkar iyaye da addu'ar su tare da yanda yake taimakon mutane yake gani saboda ganin yanda Allah yake bud'a mishi harkokin sa yana samu sosae ganin hka yasa kishi da hassada a xuciyar salisu saboda ganin sa'eed ya fishi samu ba shi kadai ba har inna larai.

   Shi kuwa bawan Allah sa'eed ba ruwan shi sau tari sai ya dauki kudi ko yayi musu d'inki tare ya bashi don yana kaunar d'an uwan shi duk da hka salisu bai fasa nuna mishi bakin cikin yafi shi samu don salisu kullum a tunanin shi yafi d'an uwan shi samu amma Allah bai bashi nasarar hkan ba.

  Safiyya kuwa dakyar baffah haruna ya barta ta gama secondary schl ya aurar da ita d'an kasuwa lokaci d'aya Allah ya had'a soyayyar su don hka da akayi bincike aka ga yana da Kyan hali ba ada'u lkc ba akayi auren aka kaita unguwar malali lfy suke xaune da mijin ta....

  Ahka lokaci yake tafiya har sa'eed ya had'u da maimuna irin kyakkyawan  nan ce don gaskia akwai ta da kyau ba k'arya 'yar ogan shi ce Allah ya had'a soyayyar su da yake ogan nashi yana son sa'eed sosae jinin su ya had'u don hka ba'a samu matsala a ko'ina ba akayi auren...

  Amarya maimuna ta tare a gidan sa'eed suna rayuwar su cikin kwanciyar hnkl hkan yasa salisu bakin ciki sosae ta yanda akayi ya auri wannan kyakkyawar kamar balarabiya tun ganin shi na farko yaji yana masifar son ta kamar me anan ya kuduri wani mugun nufi a xuciyar shi..........    *BAYAN WASU SHEKARU*............

  Abubuwa da yawa sun faru a wad'annan Shekaru Alhaji sa'eed ya samu karuwar haihuwa mata 2,safah ce ta farko sai nauwarah da batafi 3yrs ba sai tsohon cikin da take dashi haihuwa yau ko gobe...

  Ana cikin hka salisu yaxo gdn yayan shi cike da bacin rai yana shiga falon ya had'a ido da maimuna tana xaune a falon tasha kwalliya kai  ba kace ta haifi safah da nauwarah ba ae tuni yaji duk bacin ran da ya shigo dashi ya yaye washe hak'ora ya shiga yi cikin dariya yace

 " _uwar gida ran gida maman safah da nauwarah kina Lfy???_"

  Shiru tayi kamar baxa ta amsa ba saboda kwata kwata jinin su bai had'u da salisu ba ta tsane shi saboda yanda yake yiwa Baffah haruna da mijin ta sa'eed rashin kunya a dak'ile ta amsa da

  " _lfy qlau nake_"

 Bai damu da yanda take b'ata fuska ba ya samu wuri ya xauna cikin murmishi kamar mai tallan maclean yace

  " _dftn wannan siririn mijin naki ya nan Don wurin shi naxo_?

A fusace tace  " _Wannan wanne irin rashin mutunci ne salisu kaxo har gida na a gaba na kana ciwa mijina mutunci tohh wlh baxan yarda ba idan ka k'ara xan dau mataki akan ka_?

  Ranshi idan yayi dubu ya b'aci amma da yake d'an duniya ne ya k'ak'alo murmishin dole yace " _okay ayi min afuwa baxan k'ara ba matar babban yaya d'an yi min magana dashi don Allah_"

  Sai da ta saki tsaki kafin ta mik'e ta nufi stairs shi kuma ya bita da kallon yana had'yar yawu tare da lashe leb'en shi yana tunanin abubuwa da yawa a ran shi....

  Bata da deba yaji tahowar su don yana jin dariyar su k'asa k'asa alamar magana mai dad'i suke fad'a wa junan su wani abu yaji ya tokare shi a mak'wogaron shi ya fad'a tunani sai da yayan shi ya dafa mishi Kafad'a sannan ya dawo hayyacin shi ya saki wani huci mai zafi kafin ya fara magana ba alamar ma xai gaida yayan nashi yace

" _daman yarinyar da xan aura ce na samu sai old man yace bai yarda ba to nasan yafi jin maganar ka shine nake son kayi mishi magana don gaskia baxan iya hak'uri da ita ba idan yak'i yarda xan gudu a neme ni a rasa sunan yarinyar binta lawan shana_"

 Yana gama maganar ya kad'e rigar shi ya fice daga falon ya bar sa'eed kamar an dasashi a wajen cike da tunanin abin da salisu yake kok'arin janyo musu..........


   *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
  *K'ARSHEN WAHALA*🍀🍀☘☘🍀🍀
             *NA*

    *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘

*~pg 3~*Dafa mishi kafad'ar akayi da sauri ya juyo sai yayi arba da kyakkyawar fuskar matar shi tana yi mishi Murmishi amma ganin tarin damuwa a fuskar gwarxon mijin ta nan da nan fuskar ta ta rine xuwa tarin damuwa cikin muryar kwantar da hankali tace

  " _ya kai mijina menene dalilin shigar ka damuwa?_"

Kamo hannun ta yayi ya xaunar da ita kan kujera shima ya xauna yana fuskantar ta sai da ya sauke numfashi Kafin yace

   " _ba wanine ya sani shiga damuwa ba illa salisu da yake kok'arin janyo wa kanshi abin da yafi k'arfin shi?_"

 " _me yake kok'arin janyo_?"

" _wai aure yake son yi baffah bai amince da yarinyar ba shine yaxo wae baffah yafi jin magana ta nayi mishi mgn idan ba hka ba xa'a neme shi a rasa_"

Shiru tayi na d'an lokacin k'alilan tukunna ta sauke ajiyar xuciya tace

    " _idan yak'i yarda ya hak'ura da yarinyar toh ku kyale shi ya aure ta sai mu taya shi da addu'a kada ya gudu kasan xai aikata hakan_"

Shiru yayi na 'yan Mintuna Kafin yace
  " _xamu yi mgn da baffah ngde da shawarar da kika bani idan Allah ya K'addara wannan auren Shikenan fatan mu Allah ya xa6a mishi abin da yafi alkhairi amma salisu sai a hankali ya fiye rigima wlh Kinsan wacce yarinya ce kuwa?_"

Girgixa kai tayi alamar a'a " _toh 'yar gdn lawan Shana ce_"

 Zaro ido tayi Kafin ta gid'a kai tace " _Allah ya kyauta amma sam bai yi dace da mace ta gari ba_"

" _Ameeen dai amma shi ae idon shi ya rufe bae ga hkan ba_"*WANE LAWAN SHANA*

    Alhaji lawan Shana shine cikakken sunan shi don anfi sanin shi da lawan Shana sunan shana ya samo asali daga lokacin samartakar shi saboda tantirin d'an duniya ne mai son ya shana a duniya yana d'an rufin asiri ba laifi akwai masifar son yaga ya tara dukiya matan shi 4 da tarin yara har 13 gaba d'aya tarbiyyar su sae a hankali....

  Acikin su akwai wata binta Tana da kyau ba laifi sai dai maimuna tafi ta kyau nesa ba kusa ba gaba d'aya ta kwashe halin baban ta _100  percent_ shi yasa yake masifar son ta a 'ya'yan shi komai xata iya aikata wa don ta samu kud'i a kaduna polytechnic take karatu duk da bata bashi mahimmanci irin 'yan d'umama benci ne,ita ta fara cewa tana son salisu don da alama xata huta a gdn shi baya aurar da yaran shi talaka sai mai kud'i idan talaka ne mai yaci balle ya bawa 'yar shi kaji shi sai kace shi ba talakan bane ya mance Allah ne mai axurta bawan shi......


An kai ruwa rana kafin baffah ya amince don salisu akwai shi da kafe ya da hka akayi auren duk 'yan uwan shi basa so daga shi sai babar shi inna larai...

Bayan 2weeks da bikin salisu maimuna ta haihu yaro yaci suna saleem........           *******

   *MUN DAWO LABARI*

  A kayattaccen bedroom d'in su na hango nauwarah ta k'ure volume d'in tv tana jin wak'ar da deepika tayi a film d'in rasleela ram Leela kamar wadda tayi practice d'in rawar hka take yi ta iya rawar sosae kamar itace deepika d'in {lol}

 Gaba d'aya ta cikawa safah kunne da kunne da k'ara gashi karatu take saboda gobe tana da test a schl gaba d'aya tabi ta dame ta a fusace tace

  " _wannan kuma sabon wani wulak'ancin ne nauwarah ina karatu kin samu kin k'ure volume_"

Sae da ta Murgud'a mata baki Kafin tace  " _hba aunty safah don Allah ki kyale ni nayi nishad'i man Kinsan ina bala'in son wak'ar nan_"

" _ki tafi falo mana kiji_"

Zaro ido tayi tana cewa " _tabbb kina so ammi ta doke ni tana falo fah a xaune_"

Tsaki safah ta ja kafin ta tashi afusace tayi kan nauwarah da gudu tayi hanyar fita daga d'akin sai taga ashe kid'an ta kashe ta juyo Tana kallon nauwarah tayi wuk'i wuk'i da ido hararar ta tayi kafin ta juya ta xauna tana cewa

 " _sai tsabar tsokana amma tsoro fal ciki_"

Ta dauki buk d'in ta tana dubawa ganin hka yasa nauwarah ta lalla6a tana Xumbura baki taje ta jona socket d'in da safah ta kashe iya k'uluwa safah ta k'ulu ta tashi da sauri tayi kan nauwarah ae kuwa ta kwasa da gudu sai falo ita ma safah ta bita da gudu sai ganin su ammi tayi kamar wad'anda aka cillo da sauri ta mik'e Tana cewa

" _lfy safah me yafaru?_"
nauwarah tana ihun _Wayyo Mumy Ki taimaka min aunty safah xata Duke ne_"

Duk tabi ta cikawa ammi kunne da ihu gashi ta ruk'unk'u ne ta cikin fusata tace
" _ammi wannan mara kunyar yarinyar  ce ina karatu ta ishe ni da jin wak'a duk ta hanani karatu_"

Ammi tace " _baki da kunya nauwarah koh safah kike yiwa hka ba yayar ki ce ba  ki bata hak'uri kuma kada Ki sake na gaya miki_?

Cikin murya kamar xata fashe da kuka tace " _I'm so sorry my aunty safah na dai na amma kada Ki doke ni plss_"

K'wafa tayi sannan ta bar wajen nauwarah ta fito daga bayan ammi tana sakin ajiyar xuciya can kuma ta kyalkyale da dariya tace " _ohhh thank god to save me_"
Harara ammi ta watsa mata sum sum ta shige tana dariya.............


     *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀
           *NA*

   *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
*~pg 4~*


   Xaune suke a falo Alhaji salisu da Alhaji lawan sai hajia binta suna yin wasu maganganu da alama maganar da suke yi ta sirri ce ba kowa ake so yaji ba can naji muryar Alhaji salisu yana cewa
  " _ya kamata mu gama samu mafita don ni wlh na gaji da ganin shi awannan duniyar ta mu da shi da wad'annan 'yan iskar 'ya'yan nashi don ni wlh kishi nake dasu kamar yanda nake kishi da uban su_"

  Hajia binta ta xabga mishi wata harara kamar idon ta ya fad'i k'asa taja wani shegen tsaki a fusace tace

  " _wlh salisu baka da mutunci kana tunanin idan ina raye xaka auri wannan shegiyar matar mai kama da aljanu, toh wlh tun wuri kama cire son ta daga xuciyar ka idan ba hka ba sai na.................. "

 Kafin ta K'arasa fad'in hka Alhaji lawan ya daka mata wata tsawa ba shiri ta hadiye sauran maganar ta ta fuska a d'aure yace

  " _na fuskanci baku damu da abin da ya tara mu anan ba toh wlh xan tashi na tafi tunda baku tanadi abin fad'a ba,ke kuma binta idan ba rashin hankali da tunani ba ina ruwan ki da son ta da yake yi ke dai ba kud'i kike so xaki wani cikawa mutane kunne da ihu_"


Cike da rashin kunya tace " _ae bani kad'ai ce mai son kud'in ba naga Har kafi ni son su taya xae dunga maganar wannan mai kama da aljanun_"


  " _yayi d'in don uban ki tunda ke baki da mutunci ni uban Ki kike gaya wa hka ko_"

 Alhaji lawan yayi maganar a fusace har ta bud'e baki xatayi magana Alhaji salisu ya dakatar da ita da hannu Kafin ya d'ora da cewa

  " _don ynx wannan bata ta so ba ni kawai so nake a fara kawar dashi tukunna_"

Nan kowa ya fara kawo tashi shawarar idan suka duba sai aga batayi ba sun d'auki wajen _1 hour_ suna magana da K'arshe har xasu tashi da xummar kowa yaje yayi tunani akai sai har sun mik'e tsaye sai suka ga Alhaji lawan ya kwashe da dariyar mugunta ya dad'e yana dariya kafin ya tsaya su kuma suka xuba masa ido suna kallon shi cike da mamakin abin da yasa shi dariya dakyar ya tsagaita da dariyar Kafin yace

  " _kun ga ina dariya kamar na haukace ko toh mafitah na samo mana kuma mai sauk'in gaske ku kawo kunnen ku kuji saboda ina tsoron kada iska ta kwashi sauti  na aji koh yah_"

Ae kuwa da sauri suka mik'a mishi kunnen su ya d'au tsahon _10 mint_ yana magana Kafin lokaci d'aya su kwashe da wata mahaukaciyar dariya ke bakace d'an adam ne ke yi ba daga hka duk suka tarwatse xuciyoyin cike da farin ciki........         *********

   Sanye take cikin wata gown d'in shadda dark blue tasha make up Sosae tayi masifar yin kyau d'aurin d'an kwalin ya xauna a kanta sosae sai tayi amfani da sark'a white mai touch d'in blue a jiki ta sanya white shoes nauwarah kenan sarkin son gayu kenan suna masifar kama da ammin ta don ita ta kwashe kusan kyan nata don tafi safah da saleem kyau shi yasa abban su yafi k'aunar ta cikin takun ta kamar mai tausayin k'asa ta fito xuwa falo sai kace wata babbar mace don bata fi 16yrs ba a duniya amma idan tayi wani abun ka d'auka wata babbar ce.....

Kuma sunyi dace da iyaye don dai dai gwargwado sun basu tarbiyya suna da iIlimi na addini da na nasara mai jan kunnu wa Duk kud'in mahaifin su bai hana su tsaya wa k'in neman ilimi ba..

Tana k'araso wa falo ta tarar da ammi sai saleem suna xaune suna kallo cike da shagwaba ta kwanta a jikin ammi tace

 " _ammi Har ynx aunty safah Bata dawo daga schl ba_"

 " _ehhh Kinsan lectures d'in yamma ne da ita yau_"

Ammi ta bata amsa turo baki tayi gaba sannan tace  " _tabbb ammi anya xan iya kai wannan time d'in a schl kuwa ae gudu wa xanyi_"

Harar ta ammi tayi kafin tace " _daman ke ina xaki iya raguwa dake xan kuwa gaya wa abban ki kada ya b'ata kud'in shi a banxa ya kai Ki har malaysia karatu gwara ya barki anan_"

Marairaice fuska tayi tare da langab'e kai tace  " _ya hak'uri ammi na da wasa nake wlh kinsan yanda nake da burin yin karatu sosae kada ki fad'a wa abba plss_"

Dariya kawai tayi tana cewa " _ohh nauwarah ran da bamu a duniyar har tausaya miki nake wanda xai iya da shagwabar ki_"

Kicin kicin da fuska tayi can kuma sai ga hawaye yana xuba a fuskar ta cikin kuka tace  " _don Allah ammi ki dai na wannan xance ae rasa ku arayuwa ta nasan ba k'aramin *K'ARSHEN WAHALA* xan shiga ba_"

Sosae ta fashe wa ammi da kuka nan ta fara rarrashin ta tana cewa " _ae mutuwa tana kan kuwa nauwarah ba mai guje mata fatan Allah ya sa mu cika da imani_"

Dak'yar ta lalla6a tayi shiru har safah ta dawo daga schl suka cigaba da hira kiran sallahr mangariba ne ya tashe su daga hirar....


*12 pm*

 Innalillahi wa'inna ilaihir rajun ta farka a firgice daga wani mummunan mafarki da tayi gaba d'aya ta jik'e da gumi ta kai idon ta kan safah da take baccin ta hankali kwance shiru tayi tana tunanin abin da ta gani a mafarkin wai abban ta ne ya rasu gashi ana xaman makoki suna ta kuka ita dasu ammi daga nan ta fara......

Xumbur ta mik'e ta tsaye ganin an kunna hasken d'akin ido hud'u sukayi da abban ta sosae tayi mamakin ganin shi a irin wannan lokacin tashi tayi ta nufi wajen shi kawai ta tsaya kallon shi ta kasa cewa komae hannun ta ya kama ya  xaunar da ita a gefen bed sannan shima ya xauna a hankali yake magana don kada ya tashi safah a bacci yace

  " _kema Kinyi irin mafarkin da nayi ko na dad'e ina irin wannan mafarkin amma na yau yasha banban da na ko yaushe_"

Ita dai nauwarah kallon shi kawai take shima bai damu da irin kallon da take mishi ba ya cigaba da cewa

  " _ban tab'a gaya muku bane ko ammin ku bana gaya mata saboda ban son tashin hankali ku mak'iya sun yi min yawa nauwarah an dad'e ana bibiya ta don aga baya na na amma Allah bai basu ikon hkan don hka ina son ki kula da 'yan uwan ki da ammin ku, bana son ki fad'a wa kowa munyi magana dake wannan ya xama sirri a tsakanin mu_"

Nauwarah wadda ta kusan suman xaune bakin ta na rawa tace  " _Abba su wane? Kuma me suke so a wajen ka? Sannan ka fad'a wa police mana? Kuma ta yaya xan iya kula da ammi safah da saleem???_

Murmishi ya saki kafin yace "_xaki iya kula da su man sannan rayuwata da dukiya ta suke nema, hmm nauwarah ke yarinya ce shi yasa amman ae idan baka iya kama 6arawo ba shi ya kama ka sanar da police ma bata taso ba gobe xan yi tafiya xuwa kano wajen wani aminina akwai  maganar da xamu yi dashi na yarda da dashi fiye da yanda kike xato nasan baki san shi ba"

Abba ya d'an sauke numfashi Kafin ya cigaba da cewa  " _xan baki wata jaka tana d'auke da dukkan wata muhimmiyar dukiya ta don ku samu damar kula da kanku Insha Allah baxa su ci galaba a kanki ba kuma ina son idan Allah ya nufa sun samu galaba a kaina ku gudu xuwa kano xan rubuta miki address d'in shi gobe na baki nasan shi kad'ai xai iya taimaka muku tsakani da Allah_"

Hannun nauwarah ya kama ya damk'a mata wata jaka sannan ya rungume ta har sai da k'walla ta xubo mishi tashi yayi tsaye tare da cewa

" _Allah yayi muku albarka ya k'are min ku a dukk inda kuke_"

Bud'e baki nauwarah tayi xata yi mgn da sauri yasa hannu ya rufe mata baki ya nuna mata safah dake motsi  da sauri ya fice daga bedroom d'in bayan ya kashe hasken d'akin........


   *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀
             *NA*

  *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
*~pg 5~*


  Tun da abban ta ya bar d'akin take xaune cike da tsoro da tashin hankali akan abin da ya sanar da ita me yasa abban ta ya yanke hukuncin sanar da ita bai sanar da ammi da safah ba ae ita tayi k'ank'anta da asanar da mata da wannan rikitaccen labarin mai kama da film Ko mafarki *ADALILIN SON* matar shi da dukiyar shi ake neman ranshi to suwaye wad'annan marasa imanin tunanin da take da kuka su suka hassada mata matsanancin ciwon kai idon ta duk sunyi jawur dasu sai rad'ad'i suke yi mata kamar an xuba barkono


Dakyar ta iya mik'e wa tsaye ta bud'e wardrobe d'in ta ajiyar jakar tayi sannan ta nufi toilet alwala ta d'aura bayan ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo batasan adadin nawa tayi ba sai da taji jiri ya fara d'aukar ta sannan ta xauna ta janyo al qur'an ta fara karatu cikin muryar ta mai d'an karan dad'i tana hka har asuba tayi tana idar da sallah bacci yayi awon gaba da ita akan abin sallahr


Wajen 10 na safe Abba ya fito cikin shirin tafiya yasha manyan kaya farare sol dasu da yake ranar juma'a ne ya xauna akan dinning table ammi tana had'a mishi breakfast ya xuba mata ido ko kiftawa ba yayi har ta gama had'a mishi ta juyo don tayi mishi magana ta ga ya xuba mata ido yana kallon ta Murmishi ta saki wanda ya dad'a fito mata da Kyan ta kafad'ar shi ta dafa sannan tace

  " _Abban safah irin wannan kallon hka Lfy?_"

Ajiyar xuciya ya saki tare da rik'o hannun ta yace " _bakomai gani nayi yau Kinyi min kyau sosae_" dariya ya bata ta kyalkyale da dariya don wannan kalmar kullum sai ya fad'a mata dariyar da take ta bashi shima dariya don hka yayi murmishi kawai kafin tace

  " _nima kayi min kyau wlh fiye da koyaushe, amman kayi sauri ka gama don nafi son ka dawo da wuri saboda bana son dare yayi muku a hanya_"

 " _an gama ranki ya dad'e_"

A hankali ya fara cin abincin yana ci yana kallon ta tun tana jin dad'in hka har ta fara jin tsoro anya wannan kallon nashi na lfy ne kafin ta samu tayi magana safah da nauwarah sun k'araso wajen suka gaida iyayen nasu cikin girmama wa gaba d'aya nauwarah jikin ta a sanyaye yake ko gayun da ake yau babu shi ta samu waje ta xauna tare da xabga tagumi ammi ta xuba mata ido kafin tace

  " _lfy qlau kike nauwarah duk Kinyi wani iri gashi Kinxo kin xabga tagumi_"

Kafin tayi magana caraf safah tace  " _wlh umma na tambaye tun d'axu tace ba komai koh tsokana ta yau bata yi ba_"

Har ta bud'e baki xatayi magana suka had'a ido da Abba yayi mata alamar kada ki fad'a musu don hka tayi murmishi yak'e tace

  " _ammi ba komai na tashi da ciwon kai ne_"

" _Allah ya sauwake kiyi maxa ki karya sai kisha paracetamol_"

Kad'an ta iya cin abinci ta ture ta xauna har abba ya gama suka mik'e tsaye don raka shi har wajen motar da xai tafi a ciki suka rakashi duk sai da ya rungume su sannan ya shiga mota driven shi har ya kunna mota sun kusa fita daga get ya bashi umarni ya dawo baya ammi suka tsaya kallon shi cike da mamakin shi sai da ya dad'a fitowa ya rungume su ya dunga kallon su gaba d'aya sun tsorata da hkan nauwarah kuwa tuni ta fara kuka ganin hka yasa ya koma mota drive yaja mota yana ta kallon su har suka fice daga gidan gaba d'aya mai gadi ya mayar da kofa ya rufe da gudu nauwarah ta shige falo tana kuka sosae ammi da safah sai saleem suka nufi falon gaba d'aya jikin su a sanyaye dakyar suka lallashi nauwarah tayi shiru safah ta vata magani bata dad'e da sha ba bacci yayi awon gaba da ita.......


Tsaye yake a K'arshen layin da alamar jiran wani abun yake ganin wata mota ta shige yasa shi sakin wani murmishin mugunta tana shigewa ya dauko wayar shi a aljihu ya kira wata number bata dad'e tana ringing ba aka d'auka cikin wata katuwar murya yace

  " _Oga an cika aiki nan d'an lokaci xakuji kyakkyawan labari_"


Daga d'aya bangaren aka kwashe da wata mahaukaciyar dariya dakyar ya tsagaita da dariyar Kafin yace
 " _aikin ka kyau mu had'u anjima da yamma a guest house d'ina mu K'arasa biyan ka_"

Daga hka ya kashe wayar cikin farinciki ya tsayar da keken napep ya shiga suka tafi..........

  *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘
[2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀
 *K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

No comments:

Post a Comment