Wednesday, 14 November 2018

Bidiyon Da Yaja Hakulan Mutane A Wannan Satin


Wani dan karamin bidiyo da yaja hakulan mutane yake ta kai kawo a wayoyi da shafukan sada zumunta wanda kuma mutane sukai ta bayyana ra’ayoyinsu akan bidiyon wanda yajawa babban mawakin mata Ado gwanja zagi da kuma kalaman fatan Alkairee dashi da matarsa.
A kwanakin baya mutane da yawa sun san cewa ado isah gwanja wanda akafi sani da mawakin mata yayi aure wanda ya angwance tare da matarsa mai suna ” Maimunatu “.
Jarumin ya saki bidiyon a shafinsa na sada zumunta wato instagram wanda daga bisani bayan yaji korafe korafin mutane sai ya gogesa bayan mutane sun gama daukar bidiyon sun yadawa duniya shi.
Idan baku mantaba tun ana dinner bikin mutane suka dunga sharhi akan jarumin inda suka dunga zagin kanawa akan wani hoton da jarumin yayi da bluetooth a kunnensa.


Hoton Da Ya janyo Ciwa Yan Kano Mutunci A Kafafan Sada Zumunta

Video Player

No comments:

Post a Comment